Ka hakura da siyasa idan ka sha kasa a zaben 2019 - Matasan 'kabilar Ibo sun shawarci Buhari

Ka hakura da siyasa idan ka sha kasa a zaben 2019 - Matasan 'kabilar Ibo sun shawarci Buhari

Babbar kungiyar kabilar Ibo reshen Matasa ta Ohanaeze Ndigbo Youth Council, ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan hukuncin da ya kamata ya dauka yayin da ya sha kasa a babban zabe da zai gudana a ranar Asabar, 23, ga watan Fabrairu.

Kungiyar mai lakabin ONYC, ta shawarci shugaban kasa Buhari akan mika ragamar jagorancin kasar nan cikin lumana ga duk wanda ya yi nasara yayin babban zaben kasa da za a gudanar a karshen wannan mako matukar nasara ba ta rinjaya a gare sa ba.

Shugaba Buhari yayin karbar ragamar jagorancin kasar nan bayan nasarar sa a zaben 2015

Shugaba Buhari yayin karbar ragamar jagorancin kasar nan bayan nasarar sa a zaben 2015
Source: UGC

Jagoran kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro, shine ya yi furucin wannan shawara ga shugaban kasa Buhari a jiya Lahadi cikin birnin Abakaliki na jihar Ebonyi yayin wata hira da manema labarai dangane da lamari na dage babban zaben kasa.

Isiguzoro ya nemi shugaban kasa Buhari da ya yi koyi da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wanda ya sha kasa yayin babban zabe na 2015 kuma ya mika masa akalar jagorancin kasar nan cikin lumana da ruwan sanyi.

KARANTA KUMA: Dage Zabe: Jami'an tsaro za su fi kowa shan wahala - Bincike

A yayin da ake ci gaba da zargin cewa shugaba Buhari ba zai mika ragamar jagorancin kasar nan ba ko da kuwa ya sha kasa, kungiyar ONYC na ci gaba da shawartar sa akan nuna hali na dattako da karamci yayin da nasara ta juya masa baya a zaben bana.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito, a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta dage babban zabe na kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar Asabar, 23 ga watan na Fabrairun 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel