An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an samu rabuwar kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Benue.

Shugabannin jam’iyyar sun rabu ne akan kudaden da aka saki don kamfen din zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki.

An tattaro cewa hukumar zabe mai zaben kanta (INEC) ta daga zabe domin ceto APC daga shan gagarumin kaye a zaben ranar Asabar da ya gabata.

An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa

An samu rabuwar kai a APC reshen Benue kan kudaden kamfen din shugaban kasa
Source: UGC

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar sun halarci wani ganawa a jiya a City Bay Park da ke Makurdi, babbar birnin jihar domin magance matsalolin.

KU KARANTA KUMA: Dage zabe: An shawarci INEC da ta chanja takardun zabe

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a yammacin kafin ranar zabe, shugabannin APC sun yi rabon kudi a Makurdi gidan Darakta Janar na kungiyar kamfen din Jime-Ode, Cif Tilley Gyado.

An rahoto cewa an ware wasu jiga-jigan jam’iyyar wajen rabon.

Majiyoyi sun kawo cewa wasu bangare na APC sun yiwa sauran mutane wayo inda suka raba kudaden a tsakaninsu.

An tattaro cewa lamarin yayi sanadiyar kawo rabuwar kai inda wasu mambobin suka sha alwashin juya ma jam’iyyar baya a zaben da aka dage mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel