Dage zabe: Kungiyar IPMAN ta bukaci mambobinta da su rage farashin man fetur

Dage zabe: Kungiyar IPMAN ta bukaci mambobinta da su rage farashin man fetur

- Kungiyar masu siyar da man fetur na Najeriya (IPMAN) ta bukaci mambobinta dasu rage farashin man fetur daga N145 zuwa N140

- Hakan na daga cikin gudunmawar kungiyar ga yan Najeriya domin su samu damar zuwa wuraren kada kyuri'unsu sakamakon dage zaben da INEC tayi

- A ranar 23 ga watan Fabrairu ne dai za a yi zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar

Kungiyar masu siyar da man fetur na Najeriya (IPMAN) ta bukaci mambobinta dasu rage farashin man fetur daga N145 zuwa N140, wannan ya kasance daga cikin gudumawar da kungiyar zata bayar wajen karfafa masu zabe don halartan inda zasu kada kuri’a.

Wannan umurnin yazo ne a ranar Lahadi, 17 Ga watan Fabrairu daga bakin shugaban kungiyan na kasa, Elder Chinedu Okoronkwo, wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar na reshen Arewa-maso Yamma, Alhaji Bashir Salisu Tahir Kano.

Dage zabe: Kungiyar IPMAN ta bukaci mambobinta da su rage farashin man fetur

Dage zabe: Kungiyar IPMAN ta bukaci mambobinta da su rage farashin man fetur
Source: UGC

A cewar shi, shugaban kungiyar, Mista Okworonko ya bada umurnin a aiwatar da hakan ne daga ranar Laraba. Yace shawaran ya biyo bayan dage zaben shugaban kasa da na majalisa da hukumar zaben tayi a ranar Asabar.

A cewar shi, yan Najeriya sunyi tafiya zuwa waurare daban daban a fadin kasar nan don kada kuri’unsu, cikin rashin farin ciki, aka dage zaben.

KU KARANTA KUMA: INEC na bayar da katunan zabe da ba a karba ba ga APC don yin magudin zabe – PDP

Ya kara da cewa IPMAN ta rage farashin mai da naira 5 don karfafa gwiwar yan Najeriya domin su samu damar komawa garuruwansu don kada kuri’unsu a ranar 23 ga watan Febrairu da 9 ga watan Maris.

Shugaban kungiyar ya bukaci mambobi a fadin kasar dasu gaggauta aiwatar da umurnin yayinda yake tabbatar da cewa shawarar IPMAN na rage farashin mai ya kasance damuwa da kuma yunkuri na shugaban kasa Muhammadu Buhari akan daga zabe da aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel