Tashin hankali: An gano maza da mata 18 dauke da kanjamau cikin zawarawan da za'a auras a Kano

Tashin hankali: An gano maza da mata 18 dauke da kanjamau cikin zawarawan da za'a auras a Kano

Hukumar nan ta gyaran dabi'u watau Hisba ta jihar Kano dake a Arewa maso yammacin Najeriya tace ta soma tantance kimanin akalla maza da mata dubu takwas a cikin shirin nan nata na aurar da zawarawa da gwamnatin jahar ta shirya.

Tun a ranar 12 ga watan Disambar 2018 ne dai gwamnatin jahar ta kafa wani kwamitin mai mutun 23 domin tantance wadanda ake son aurarwa. An dai ware aurar da 3000 daga cikin 8,000, bayan gano maza da mata 18 dauke da cutar HIV da kuma ciki.

Tashin hankali: An gano maza da mata 18 dauke da kanjamau cikin zawarawan da za'a auras a Kano

Tashin hankali: An gano maza da mata 18 dauke da kanjamau cikin zawarawan da za'a auras a Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Hon. Abdulmumini Jibrin ya yi hasashen wanda zai lashe zaben 2019

Shugaban Kwamitin aurar da zawarawan Ali baba Fagge a gama lafiya ,ya shaidawa BBC cewa gwamnati ta debo litoci daga asibiti jihar da na tarayya domin gudanar da aikin tantacewar don kaucewa fasa gurbi.

A cewarsa, matasa da dama na bukatar aure, amma rashin sukuni ya hana su, don haka ne ake tallafa musu.

Ya ce an ware masu dauke da cuta mai karya garkuwa jiki, kuma an daura su aka maganin, sannan an bukaci masu dauke da irin cutar idan su amince da juna ko kuma suna da mai son su a haka su gabatar da su sai a hada auren su.

Ali Baba ya ce akwai kalubalen da suke fuskanta saboda a wasu lokutan mata na gujewa shiga tsarin aurar da zawarawan saboda wasu dalilai da suka danganci al'ada da dai sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel