Dage zabe: An shawarci INEC da ta chanja takardun zabe

Dage zabe: An shawarci INEC da ta chanja takardun zabe

- Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Kwara, Yakubu Gobir, ya shawarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta canja takardun zabe na shugaban kasa da majalisar dokokin kasa

- Gobir ya kuma shawarci hukumar zaben da ta sanya tsarin tsaro saboda ta kau da duk wani nau’in mirdiya

- Ya kuma kara da cewa da hukumar tayi amfani da NSPMC a madadin kamfanoni bugun takardun zabe na gida da sauran kayan zabe na gida

Wazirin Hausawa kuma baban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kwara, Yakubu Gobir, ya shawarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta canja takardun zabe don gujewa murdiya.

Haka zalika, Gobir ya bayyana cewa dage zaben shugaban kasa da na majalisa da hukumar zaben tayi ba tare da zatto ba ya nuna cewa damokardiyyan kasar Najeriya bata yi kwari ba ko.

Dage zabe: An shawarci INEC da ta chanja takardun zabe

Dage zabe: An shawarci INEC da ta chanja takardun zabe
Source: Original

Jigon jam’iyyar ya shawarci hukumar zaben da ta canja takardun zabe gaba daya sannan ta sanya tsarin tsaro saboda ta kau da duk wani nau’in mirdiya, ya kuma kara da cewa da hukumar tayi amfani da NSPMC a madadin kamfanoni bugun takardun zabe na gida da sauran kayan zabe na gida.

Yayi zargin cewa wasu jam’iyyun siyasa sun kashe biliyoyin nairori kafin zaben ranar Asabar don siye kuri’u wanda a ganinsa, zai yi wuya kafin hukumar ta sake sanya sabon kwanan wata na zabuka.

KU KARANTA KUMA: INEC na bayar da katunan zabe da ba a karba ba ga APC don yin magudin zabe – PDP

Yayi tuni ga hukumar zabe cewa an zura mata ido kamar yanda ake tsammanin ganin yanda tarihi zata fassara Farfesa Mahmoud Yakubu tare da tawagarsa kamar yanda lamarin siyasa a kasar ke cigaba da gudana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel