INEC na bayar da katunan zabe da ba a karba ba ga APC don yin magudin zabe – PDP

INEC na bayar da katunan zabe da ba a karba ba ga APC don yin magudin zabe – PDP

- Jam'iyyar PDP reshen Edo ta zargi hukumar INEC da ba APC katunan zaben wadanda basu karbi nasu ba

- PDP tace hakan wani yunkuri ne da jam'iyya mai mulki ke yi don magudin zabe

- Sai dai daga INEC har APC sun karyata wannan zargi cewa makircin jam'iyyar adawa ne kawai

Shugaban Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Edo yayi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na bayar da dubban katunan zabe da masu shi basu karba ba ga mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) cikin sirri domin yin magudi a zaben kasar.

Sai dai kuma a lokacin da aka tuntube shi a wayar tarho, kwamisinan zabe (REC), Mista Emmanuel Alex-Hart yace “ba gaskiya bane.”

INEC na bayar da katunan zabe da ba a karba ba ga APC don yin magudin zabe – PDP

INEC na bayar da katunan zabe da ba a karba ba ga APC don yin magudin zabe – PDP
Source: Depositphotos

Shugaban masu wayar da kan masu zabe a hukumar INEC na jihar, Mista Timidi Wariowei ya bayyana cewa akalla katunan zabe 2, 219, 778 aka karba daga hedkwatar INEC inda 483,868 kawai ne masu shi basu karba ba.

Babban sakataren labarai na APC a jihar, Mista Chris Azebamwan ma ya karyata zargin inda yace lallai hakan wani yunkuri ne na jam’iyyar adawa don ganin ta hargitsa tsarin, bayan ta zan cewa zata fadi.

KU KARANTA KUMA: Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

A cewar Azebamwan, zargin abun dariya nedomin akwai tsare-tsare uku da suka hada da tabbatar da katin zabe a na’urar tantance masu zabe, duba sunfurin yatsu da kuma sunayen masu zabe akan rijista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel