Tsuguni bata kare ba: Gungun yan bindiga sun halaka mutane 3 da Soja 1 a jahar Katsina

Tsuguni bata kare ba: Gungun yan bindiga sun halaka mutane 3 da Soja 1 a jahar Katsina

Wasu gungun yan bindiga sun halaka mutane uku da basu ji ba, basu gani ba, tare da wani jami’in rundunar Sojan kasan Najeriya, a yayin wani hari da suka kai kauyen Kasai dake cikin karamar hukumar Batsari ta jahar Katsina.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne da misalin karfe daya na daren Lahadi, inda yan bindigan suka jikkata mutane da dama a kauyen, sa’annan suka kora sama da shanu dari biyu.

KU KARANTA: Aiki na kyau: Wasu gungun gagga gaggan yan fashi da makami sun fada komar Yansanda

Sai dai rahotanni sun bayyana koda yan bindigan suka afka kauyen suna harbe harbe, sai da jama’an kauyen suka taresu inda aka yi ta bata kashi, amma daga bisani suka fi karfin jama’an kauyen, daga baya kuma Sojoji suka isa.

Da yake tsokaci kan harin, kaakakin rundunar Yansandan jahar Katsina, Gambo Isah ya tabbarar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun fito ne daga dajin Rugu dake tsakanin kananan hukumomin Safana da Dutsanma.

A cewarsa sai bayan sun kai ma kauyen hari, sa’annan suka yi ma Sojojin da aka tura kwantan bauna, a haka suka kashe jami’in Soja guda daya, amma yace tuni kwamishinan Yansandan jahar, Sunusi Buba ya kai ziyarar gani da ido zuwa kauyen, tare da taya jama’an kauyen alhini.

Sai dai kaakakin ya musanta rahoton dake cewa yan bindigan sun yi awon gaba da shanu sama da dari biyu, amma ya tabbatar da cewa yan bindigan sun afka gidajen jama’a da dama inda suka kwashe kudade da wayoyin salula.

Daga karshe yace kwamishinan Yansandan ya tura da karin jami’an tsaro zuwa kauyen domin karfafa tsaro don gudun sake aukuwar lamarin anan kusa, tare da tabbatar da tsaron lafiyan jama’an kauyen da dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel