Aiki na kyau: Wasu gungun gagga gaggan yan fashi da makami sun fada komar Yansanda

Aiki na kyau: Wasu gungun gagga gaggan yan fashi da makami sun fada komar Yansanda

Jami’an rundunar Yansandan jahar Enugu sun samu nasarar cafke wasu gungun gagga gaggan yan fashi da makami guda hudu da suka gagara a jahar Enugu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Ebere Amaraizu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar dake garin Enugu, a ranar Lahadi, 17 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

A jawabinsa, Kaakaki Ebere yace Yansanda sun kama yan fashin ne da misalin karfe 10:30 na daren Asabar bayan samun wasu bayanan sirri game da ayyukan gungun yan fashin, wanda ya bayyana sunayensu kamar haka;

Uchenna Okwor inkiya Selepete, Chinonso Nnamani inkiya Okochi, Sopuruchukwu Odono inkiya Carton da kuma Kosarachi Anike. Bugu da kari kaakakin yace sun kwace bindiga guda daya daga hannun yan fashin.

“Mun samu nasarar cafkesu ne bayan samun rahoton sun kai ma wani mutumi wanda shine manajan wani kamfanin kiwon kaji dake Akpouga Nike hari a ranar Asabar, inda suka nuna masa bindiga suka kwace masa kudi N110,000, sa’annan suka jikkata direban Keke Napep dake dauke da shi.” Inji shi.

Daga karshe dai kaakaki Ebere yace yan fashin sun tabbatar da aika laifukan kai hare hare na kungiyoyin asiiri, kuma da zarar sun kammala gudanar da bincikensu zasu gurfanar dasu gaban kotu domin samun hukuncin daya dace dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel