Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

Tsatsttsamar dangantaka ta kunno kai tsakanin gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello da mataimakinsa Cif Simon Achuba, wanda har a yanzu ta kai ga gwamnan ya janye ma mataimakin jami’an tsaron dake gadinsa, sa’annan ya dakatar da albashinsa da sauran hakkokinsa.

Legit.ng ta ruwaito Cif Achuba da kansa ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 17 ga watan Feburairu, inda yace tun a ranar Juma’ar data gabata yansandan dake gadinsa suka amsa kiran babban mai gadin gwamnan jahar zuwa fadar gwamnatin jahar, daga nan basu sake dawowa ba.

KU KARANTA: Shekaru ya shirya taron gabatar da addu’o’I na musamman game da zaben gobe

Ku kawo min dauki, Gwamna na neman kassara ni – Inji Mataimakin Gwamnan jahar Kogi

Yahaya Bello da Achuba
Source: UGC

“Yayin da Yansandan dake gadina suka isa fadar gwamnatin sai aka zarce dasu ofishin Yansandan SARS da nufin su bada bayani game da tuhumar da ake musu na badakalar sayar da bindigu da makamai, har yanzu garkame a fadar gwamnatin.

“Na kai korafi ga kwamishinan Yansandan jahar, amma ya bayyana min yana sane da maganar, amma har yanzu ya gagara daukan wani kwakkwaran matakin ganin an sakosu, domin kuwa sharri ake musu, bita da kulli ake min.” Inji shi.

Mataimakin gwamna Achuba ya cigaba da kokawa yana cewa “A matsayina na dan jam’iyyar APC na kai korafi ga shugaban jam’iyyar akan cewa Gwamna Yahaya Bello ya dakatar da albashina da sauran hakkokina, hakan ba tare da wata hujja ba.

“A yanzu haka ina zaune a gidana bani da tsaro, ina tafiye tafiye duk ba tare da jami’an tsaro ba, wannan ya tabbatar da cewa rayuwata na cikin hadari, gwamnatin jahar Kogi ta yanke wutan lantarkin gidana, ta yanke ruwan famfona ma.” Inji shi.

Sai dai da aka tuntubi kwamishinan Yansandan jahar game da matsalar rashin tsaronsa da Achuba ya yi, sai yace zai tura masa sabbin jami’an Yansanda guda biyu zuwa gidansa domin bashi tsaron daya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel