Tinubu ya so APC ta tsaida wani mutum dabam a matsayin Sanatan Legas ta takiya

Tinubu ya so APC ta tsaida wani mutum dabam a matsayin Sanatan Legas ta takiya

Babban jigo na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa yayi kokarin hana Mai dakin sa watau Sanata Oluremi Tinubu komawa kujerar da ta ke kai a zaben da aka yi bana.

Tinubu ya so APC ta tsaida wani mutum dabam a matsayin Sanatan Legas ta takiya

Tinubu bai so Matar sa ta lashe zaben fitar da gwani a APC ba
Source: UGC

Tsohon gwamnan na Legas wanda Matar sa ta ke wakiltar jihar a majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa wasu a APC ne su kayi kutun-kutun na ganin Mai dakin sa ta koma majalisa a 2019 bayan yayi kokarin hanawa.

Bola Tinubu yake cewa da farko yayi kokarin hana duk wani Sanatan Legas da ke neman komawa majalisa a karo na uku samun tikiti a APC. A haka ne dai Bayo Osinowo ya tika Gbenga Ashafa da kasa a zaben tsaida ‘dan takara.

KU KARANTA: Ban da wani shiri na tsige shugaban hukumar INEC - Buhari

Jigon na APC yake fadawa wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar da su ka ziyarce sa kwanan nan daga Mazabun jihar Legas cewa yayi yunkurin a hana Mai dakin sa samun tikiti a jam’iyyar APC amma Mista Prince Tajudeen Olusi ya tsaya mata.

Tajudeen Olusi yana cikin kusoshin APC na jihar Legas Kuma yana cikin majalisar GAC wadanda ke juya siyasar jihar. Tinubu yace Prince Olusi da wasu manyan APC ne su ka matsa masa cewa dole a bar Remi Tinubu ta sake zarcewa.

Jigon jam’iyyar na kasa yake cewa da an bi ta shi, da Remi Tinubu ba ta samu tutar takara a APC ba. Asiwaju Tinubu yace ya so a ce ne APC ta tsaida wani sabon jini wannan karo daga Legas ta tsakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel