Akwai bukatar Mutanen Najeriya su san yadda ake ciki game da zabe – APC

Akwai bukatar Mutanen Najeriya su san yadda ake ciki game da zabe – APC

- APC mai mulki tayi wasu kira ga Hukumar INEC game da zaben 2019

- APC tana so a sanar da jama’a ko duk kayan zabe sun shigo Najeriya

- Jam’iyyar ta nemi ayi wa Duniya bayanin abin da ya sa aka dage zabe

Akwai bukatar Mutanen Najeriya su san yadda ake ciki game da zabe – APC

Jam'iyyar APC tana so ta ji irin tanadin da INEC ta ke yi a kasa
Source: Depositphotos

Mun ji labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta mika wasu jerin bukatun ta na musamman ga hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC game da babban zaben da za a gabatar a cikin kwanan nan.

Wani kwamiti mai kula da sha’anin zabe a jam’iyyar ta APC ta nemi hukumar INEC ta rika gudanar da sha’anin ta a bayyane ke-ke-da-ke-ke. Shugaban wannan kwamiti na APC watau Babatunde Fashola ya fadi wannan.

KU KARANTA: Buhari ne zai lashe zaben 2019 da gagarumin rinjaye - Inji Jibrin

Darektan kwamitin kula da hakar zaben na APC, Raji Fashola, yayi wannan bayani ne lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a Ranar Lahadi bayan an dakatar da zaben kasar sai zuwa wani mako bayan an sa ran cewa za a gudanar da zaben.

Jam’iyyar APC ta lissafo abubuwan da ta ke nema daga wajen hukumar INEC kafin ranar da aka sa za ayi zabe. Wadannan manyan abubuwa dai da Raji Fashola wanda Minista ne a gwamnatin shugaban kasa Buhari ya ambata su ne:

1. A rika bayyanawa Duniya inda aka kwana a wajen shirye-shiryen zaben

2. A sanar da jama’a ko kayan zabe sun iso Najeriya

3. Jama’a su samu labarin tsarin raba kayan aikin zaben a sassan kasar nan.

4. A bayyanawa mutane hanyar da za a bi wajen jigilar kayan aikin zaben.

5. Tsarin da hukumar INEC da CBN su ka shirya na adana kayan zabe.

6. A tabbatar na’urorin tantance masu kada kuri’a su na kan bakin aiki.

7. Sannan kuma a rika yi wa mutanen kasa bayani a duk rana ta Allah game da inda aka kwana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel