PDP ta rubutawa INEC wasika tana neman a binciki na’urorin tantance kuri’a

PDP ta rubutawa INEC wasika tana neman a binciki na’urorin tantance kuri’a

Mun samu labari cewa jam’iyyar adawa ta PDP, ta aika takarda ga hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta na INEC game da kwangilar shigo da na’urorin da ake amfani da su wajen aikin zabe a Najeriya.

PDP ta rubutawa INEC wasika tana neman a binciki na’urorin tantance kuri’a

Jam'iyyar PDP ta nemi INEC ta tantance ingancin na'urorin ta
Source: Twitter

Kwanan nan ne mu ka samu labari cewa kamfanin da aka ba jigilar shigo da kayan zabe a Najeriya, na wani mutumi ne wanda yake neman takarar kujerar Sanata a jam’iyyar APC mai mulki, don haka PDP tace a sake duba lamarin.

Shugaban jam’iyyar hamayyar ta PDP, Uche Secondus, ya aikawa hukumar zabe na INEC wasika inda ya nemi ta binciki kwangilar shigo da na’urar tantance masu kada kuri’a watau “Card Reader” da aka ba kamfanin wani ‘Dan APC.

Secondus, ya aikawa shugaban hukumar na INEC watau Farfesa Mahmood Yakubu da takarda ne jiya Lahadi yana neman a yi bincike na musamman game da kwangilar da aka ba Muhammad S. Musa na shigo da wasu kayan zabe.

KU KARANTA: 'Dan APC ne ya yi kwangilar kayan aikin zabe – Shugaban INEC

Shugaban na PDP ya bada shawarar ayi amfani da wasu kamfanoni na dabam masu zaman kan-su wajen binciken kayan zaben da za ayi aiki da su domin ayi adalci. Secondus ya rubuta takardar ne a madadin ‘dan takara Atiku Abubakar.

PDP ta nemi a soke kwangilar da aka yi da wannan kamfani saboda ganin cewa mai kamfanin yana takara a zaben 2019. Jam’iyyar hamayyar tana ganin idan haka ba zai yi yiwu ba, akalla ayi bincike domin tabbatar da inganci na’urorin kafin zabe.

Ita dai hukumar zabe tana ganin cewa don an ba kamfanin wani mai neman takarar Sanata a APC kwangilar aikin zaben, hakan ba zai kawo matsala ko rashin inganci a zaben da za a gudanar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Online view pixel