Ba bu wani shiri na tsige shugaban hukumar INEC - Fadar Shugaban kasa

Ba bu wani shiri na tsige shugaban hukumar INEC - Fadar Shugaban kasa

A sakamakon dambarwa da ta biyo bayan dage babban zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta yi a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2019, ana ci gaba da cece kuce dangane da daukan hukunci akan shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu.

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, fadar shugaban kasa a jiya Lahadi ta yi karin haske dangane da matakin da za ta dauka kan shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, sakamakon dage babban zabe kwatsam sa'o'i kadan gabanin gudanar sa.

A yayin da ake ci gaba da babatu da bayyana ra'ayoyi kan hukunci ko kuma rashin sa akan shugaban hukumar, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce ba ta da wani nufi na tsige Farfesa Yakubu sabanin yadda ake kiraye-kiraye da zargi akan hakan.

Shugaban INEC; Farfesa Mahmood Yakubu yayin bayar da sanarwar dage babban zaben kasa
Shugaban INEC; Farfesa Mahmood Yakubu yayin bayar da sanarwar dage babban zaben kasa
Source: UGC

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, jiga-jiga 'yan siyasa musamman daga bangaren masu adawa da gwamnatin shugaba Buhari na ci gaba da kiraye-kirayen tsige shugaban INEC sakamakon rikon sakainar kashi da kujerar sa ta jagoranci.

Babban hadimi ga shugaban kasa akan hulda al'umma, Mallam Garba Shehu, shine ya yi karin haske kan wannan lamari da ke ci gaba da gudana a kan harsunan al'ummar kasar nan. Mallam Garba ya ce ba bu kamshin gaskiya akan zargi na tsige Farfesa Yakubu.

KARANTA KUMA: Gwamna Yari ne ya kulla kutungwilar dage zaben kasa - Sanata Marafa

Da ya ke musanta wannan zargi, hadimin shugaban kasar cikin kaushin harshe ya jingina rashin ilimi ga masu zargin cewa shugaban kasa zai tsige Farfesa Yakubu ba tare da bibiyar tafarki na kundin tsarin mulkin kasa ba.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, karin haske na fadar shugaban kasa ya biyo bayan zargin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da kuma kungiyar jam'iyyun hadin gwiwa ta CUPP, da su ka yi ikirarin cewa shugaba Buhari ya daura damara ta tsige shugaban hukumar INEC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel