Buba Galadima yayi kaca-kaca da Buhari yace ya sabawa alkawarin da ya dauka

Buba Galadima yayi kaca-kaca da Buhari yace ya sabawa alkawarin da ya dauka

Mun samu labari cewa Buba Galadima, wanda yana cikin masu magana a madadin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar yayi magana game da batutuwan da su ka shafi zaben da za ayi kwanan nan.

Buba Galadima yayi kaca-kaca da Buhari yace ya sabawa alkawarin da ya dauka

Galadima yace Buhari bai da koshin lafiya don haka a zabi jam’iyyar PDP
Source: Depositphotos

Injiniya Buba Galadima yayi wata hira wanda ta shigo hannun NAIJ Hausa inda ya bayyana cewa duk wanda ya zabi shugaba Muhammadu Buhari, ya san cewa mataimakin sa watau Yemi Osinbajo kurum ya sakawa kuri’a ba kowa ba.

Galadima wanda a da yake tare da Buhari ya dai karyata cewa ya juyawa gwamnatin APC baya ne don an hana sa kujerar Minista. Dattijon yana ganin cewa idan ma za a duba sakayya, ya cancanci shugaba Buhari ya ba sa wani mukami.

KU KARANTA: Buba Galadima ya yi wa ubangiji izgili saboda zaben 2019

Dattijon yace Buhari bai cika alkawuran da ya dauka a baya ba domin harkar tsaro ya sake tabarbarewa a mafi yawon jihohin kasar nan, sannan kuma tattali ya rushe. Galadima yace tun daga taron Kano, APC ta san cewa ta fadi zabe.

Alhaji Galadima kuma karyata surutun da ake yi na cewa Diyar sa tana aiki a Aso Villa, yace idan har da gaske ne a fadi mukamin ta. Galadima yace shi Buhari da kan sa ne ya bada auren Diyar nan ta sa kuma tana da Digiri har 5.

Tsohon Sakataren na jam’iyyar CPC wanda ta narke cikin APC ya kuma bayyana cewa babu wani aikin a zo a gani da Buhari ya tabuka musamman a Arewacin Najeriya don haka ya nemi a zabi Atiku Abubakar domin ya gyara kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel