Dage zabe: An samu sabani tsakanin shugaban INEC da wani ministan Shugaba Buhari

Dage zabe: An samu sabani tsakanin shugaban INEC da wani ministan Shugaba Buhari

Wasu bayanai da ke fitowa a 'yan awannin da suka gabata sun nuna cewa akwai rabuwar kai da kuma sabanin fahimha a tsakanin shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta kasa watau INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da ministan Sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.

Mun samu dai cewa shugaban na INEC da yake bayyana dalilan da ya sa hukumar sa ta dage gudanar da zaben shugaban kasa da sati daya, yace hadda matsalolin yanayi da hazo wanda yace ya safi jigilar kayayyakin zaben su ta jiragen sama.

Dage zabe: An samu sabani tsakanin shugaban INEC da wani ministan Shugaba Buhari

Dage zabe: An samu sabani tsakanin shugaban INEC da wani ministan Shugaba Buhari
Source: Instagram

KU KARANTA: Hotunan kafin auren Sadiq Sani Sadiq da Rahama Sadau sun tayar da kura

Sai dai da yake mayar da martani akan hakan, Ministan sufurin Sanata Sirika ya musanta hakan a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sa na dandalin sada zumuntar zamani ta Tuwita da ranar yau.

A cikin sakon da ya wallafa, Sanata Siriki ya shawarci shugaban na INEC da ya sake wani uzurin amma ba rashin kyawon yanayin sufurin jirage ba domin a cewar sa ranar ba'a samu hazo ba kamar yadda shugaban ya bayyana kuma dukkan filayen jiragen saman kasar a bude suke.

A wani labarin kuma, kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ma su zaman kan su (IPMAN) ta bawa dukkan mambobinta rage farashin litar man fetur daga N145 zuwa N140 domin rage wa ma su zabe radadin daga zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta yi.

Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Chinedu Okoronkwo, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a yau, Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel