Dage zabe: IPMAN ta bayar da umarnin rage farashin man fetur

Dage zabe: IPMAN ta bayar da umarnin rage farashin man fetur

Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ma su zaman kan su (IPMAN) ta bawa dukkan mambobinta rage farashin litar man fetur daga N145 zuwa N140 domin rage wa ma su zabe radadin daga zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta yi.

Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Chinedu Okoronkwo, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a yau, Lahadi.

Mista Okonkwo ya ce mambobin kungiyar su za su fara aiki da wannan sabon umarni daga ranar Laraba, 23 ga watan Fabarairu.

Ya ce kungiyar ta yanke wannan shawara ne domin ma su kada kuri’a su samu sukunin yin bulaguro ya zuwa wuraren sana’o’in su da su ka bari domin zuwa garuruwan su domin kada kuri’u a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya amma kuma aka daga zaben.

Dage zabe: IPMAN ta bayar da umarnin rage farashin man fetur

IPMAN ta bayar da umarnin rage farashin man fetur
Source: UGC

A cewar sa, kungiyar IPMAN ta zabtare farashin man fetur din ne zuwa N140 domin kar jama’a su fasa koma wa garuruwan su domin kada kuri’a a zaben da za a yi a ranar 23 ga wata.

Mu na kira ga dukkan mambobin mu da ke fadin kasar nan da su gaggauta rage farashin litar man fetur daga N145 zuwa N140.

DUBA WANNAN: Zabe: Buba Galadima ya yi wa ubangiji izgili, bidiyo

“mun yi hakan saboda halin da aka tsinci kai a kasa bayan INEC ta daga zaben shugaban kasa da mambobin majalisar tarayya bayan ‘yan Najeriya sun kamala shirin fita domin kada kuri’a.

“Mu na sane da cewar ‘yan Najeriya sun yi bulaguro ya zuwa garuruwan su domin su yi zabe amma katsam aka daga zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu," a kalaman Okonkwo.

Shugaban ya bukaci mambobin su da su gaggauta kaddamar da wannan umarni na uwar kungiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel