Aratabu: 'Yan Boko Haram sun yiwa sojojin Najeriya kwanton bauna, sun kashe 4

Aratabu: 'Yan Boko Haram sun yiwa sojojin Najeriya kwanton bauna, sun kashe 4

Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan kungiar Boko Haram sun kashe jami'anta hudu lokacin da suka yi yunkurin kutsa kai sansanin sojin da ke jihar Yobe ranar Asabar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar na riko Kanar Sagir Musa ya aike wa manema labarai ta ce lamarin ya faru ne a sansanin sojin da ke Buni Yadi a karamar hukumar Gujba.

Aratabu: 'Yan Boko Haram sun yiwa sojojin Najeriya kwanton bauna, sun kashe 4

Aratabu: 'Yan Boko Haram sun yiwa sojojin Najeriya kwanton bauna, sun kashe 4
Source: Twitter

KU KARANTA: Zan duba yiwuwar yafewa barayi - Atiku

A cewarsa, sojoji sun kashe mayakan Boko Haram biyar a yayin arangamar da suka yi.

"Abin takaici shi ne, babban jami'in soja daya da kuma kananan sojoji uku sun rasa rayukansu lokacin arangamar. Kazalika sojoji biyar sun samu raunuka, ko da yake suna samun sauki bayan an duba lafiyarsu", in ji Kanar Sagir Musa.

Kakakin rundunar sojin na riko ya ce dakarun sojin sun kwace makamai da dama daga wurin mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Wannan hari shi ne na baya bayan nan da mayakan Boko Haram suka kai a yunkurin da suke yi na kwace sansanin sojin kasar.

Da ma dai mayakan sun mayar da hankali wajen kai hari a sansanonin soji, lamarin da masu sharhi kan sha'anin tsaro ke ganin abin tayar da hankali ne ganin kwarewar da soji ke da ita.

Sun kara da cewa 'yan Boko Haram sun fito da wannan salo na kai hari kan sansanin soji ne domin bai wa 'yan kasa tsoro da kuma nuna musu cewa su kansu sojojin ba su tsira ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel