Gwamna Yari ne ya kulla kutungwilar dage zaben kasa - Sanata Marafa

Gwamna Yari ne ya kulla kutungwilar dage zaben kasa - Sanata Marafa

- Sanata Kabiru Marafa ya ce gwamna Abdulaziz Yari ne ya kulla duk wata kitimurmura da ta yi sanadiyar dage babban zaben kasa na 2019

- Sanatan na jam'iyyar APC ya ce gwamnan jihar Zamfara ke da alhakin kulla duk wata kutungwila da ta hadda sauya ranakun gudanar da babban zabe

- Sanata Marafa ya hikaito wani kalami na gwamnan Yari da ya zayyana cewa zabe ba zai gudana ba cikin kasar nan matukar hukumar INEC ba ta bayar da amince da 'yan takarar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ba

A jiya Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta dage babban zabe kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ta shirya aiwatarwa a wannan mako.

Hukumar INEC ta dage zaben zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu, yayin da ta dage zaben gwamnoni da na 'yan majalisar tarayya daga ranar 2 ga watan Maris zuwa ranar 9 ga watan na wannan shekara da muke ciki.

Sanata Kabiru Marafa

Sanata Kabiru Marafa
Source: Twitter

Jagoran kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kwararar man fetur, Sanata Kabiru Marafa, ya yi karin haske dangane da wanda ya kulla kutungwila da kuma kitimurmurar da ta yi sanadiyar dage babban zaben kasa.

Sanata Marafa wanda shine wakilin shiyyar Zamfara ta Tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya, ya yi zargi da cewa gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ke da alhakin kulla kitimurmurar da ta haddasa dage babban zaben kasar nan.

Sanatan na jam'iyyar APC ya hikaito wani kalami na gwamna Yari da ya zayyana cewa, zabe ba zai gudana ba cikin kasar nan muddin hukumar INEC ba ta amince da 'yan takarar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ba.

KARANTA KUMA: Dage Zabe: INEC ta tabbata zabe ya gudana a mako mai zuwa - Amurka

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, 'yan takarar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar fushin hukumar INEC na rashin amincewa da takarar su sakamakon sabawa dokokin ta yayin zaben fidda gwani da suka gudanar a shekarar da ta gabata.

Sanata Marafa ya yi kira da dukkanin hukumomin tsaro ma su ruwa da tsaki da suka gaggauta cikwiye kugun Gwamna Yari tare da makarraban sa da suka shiga kuma suka fita wajen kulla kutungwilar dage babban zaben kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel