Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC ta kira taron gaggawa

Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC ta kira taron gaggawa

- Jam'iyyar APC ta kira taron gaggawa biyo bayan dage zabe da INEC tayi

- Za a gudanar da taron ne a safiyar ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu

- Wata majiya mai karfi a jam’iyyar ta bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da dage zaben wajen sake duba manufofin da za ta yi amfani dasu wajen yin nasarea a zabe mai zuwa

Biyo bayan dage zaben kasar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tayi, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta shirya gudanar da wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu, jartifdar Vanguard ta ruwaito.

Sabanin yadda aka saba gudanarwa a fadar shugaban kasa, taron wanda aka shirya gudanarwa da karfe 11:00 na safe zai gudana ne a sakatariyar jam’iyyar.

Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC ta kira taron gaggawa

Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC ta kira taron gaggawa
Source: Twitter

Wata majiya mai karfi a jam’iyyar ta bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da dage zaben wajen sake duba manufofin da za ta yi amfani dasu wajen yin nasarea a zabe mai zuwa.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyar APC, a jihar Rivers ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da ta tabbata ta sanya 'yan takararta a cikin wadanda za su fafata a zabukan jihar, tana mai cewa bijirewa wannan bukatar zai jawo asarar zaben jihar, kuma tilas ne ga hukumar ta sake wani sabon zabe.

KU KARANTA KUMA: Dage zabe zai kawo cikas ga amincewa da kasafin 2019 — Majalisar dokoki

A kokarinta na ganin hukumar ta cika wannan bukatar tata, jam'iyyar ta ce wakilanta daga jihar Rivers sun shigar da kararraki akan shugaban hukumar ta INEC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel