Dage zabe zai kawo cikas ga amincewa da kasafin 2019 — Majalisar dokoki

Dage zabe zai kawo cikas ga amincewa da kasafin 2019 — Majalisar dokoki

Majalisar dokokin Najeriya ta ce dage zaben da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi ya shafi wasu bukatu masu matukar muhimmanci da ke gabanta.

Kakakin majalisar wakilai Hon. Abdurrazaq Namdaz ya bayyanawa manema labarai cewa dage zaben zai yi matukar illa ga ayyukan majalisa musamman batun amincewa da kasafin kudin 2019 da kuma wasu muhimman bukatu da ke gabansu.

"Dage zaben ya mayar da hannun agogo baya, musamman kasafin kudin Najeriya na 2019 da ke jiran amincewar majalisa," cewar shi.

Dage zabe zai kawo cikas ga amincewa da kasafin 2019 — Majalisar dokoki

Dage zabe zai kawo cikas ga amincewa da kasafin 2019 — Majalisar dokoki
Source: UGC

Hukumar zaben Najeriya INEC ta nemi afuwar 'yan kasar bayan dage zaben da aka shirya gudanarwa na shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya a ranar Asabar.

Hukumar ta ce ta dage zaben ne saboda matsaloli na kai kayan zabe da wuri a wasu jihohi takwas daga cikin 36 na Najeriya.

Mista Namdaz ya ce yanzu ba su da tabbas ko za su koma zama a ranar Talata kamar yadda suka shirya saboda dage zaben da ya shafe su matsayinsu na 'yan majalisa kuma 'yan takara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jam’iyyar APC ta kira taron gaggawa

Ya ce 'yan majalisa ba su ji dadin dage zaben ba saboda sun yi kokari wajen amincewa da dukkanin bukatun hukumar zaben kasar domin gudanar da ayyukanta cikin lokaci.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa majalisar dokokin kasar ta sanar da dage ranar dawowarta zama wacce ta shirya yi a ranar Talata 19 ga watan Fabrairu zuwa ranar Talata 26 ga watan Fabrairu.

Magatakardar majalisar dokokin kasar, Mista Mohammed Sani-Omolori ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Lahadi, 17 ga watan Fabrairu.

Yace akwai bukatar daga dawowa majalisar sakamakon dage ranar zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da aka daga zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel