Babbar magana: CUPP ta umurci jam'iyyun da ke karkashinta da su ci gaba da yakin zabe

Babbar magana: CUPP ta umurci jam'iyyun da ke karkashinta da su ci gaba da yakin zabe

- Kungiyar CUPP ta umurci jam'iyyun da ke karkashin ta da su ci gaba da gangamin yakin neman zabensu, la'akari da sashe na 99 da ke cikin kundin dokar zabe

- Kungiyar hadakar jam'iyyun siyasa na kasar ta ce har sai ranar Alhamis, 21 ga watan Fabreru ne doka ta rufe yakin zaben

- CUPP ta ce zai zama ba dai-dai ba idan har jam'iyyun siyasa suka dakatar da yakin zabensu a ranar 14 ga watan Fabreru alhalin za a fara jefa kuri'a a ranar 23 ga wata

Kungiyar hadakar jam'iyyun siyasa na kasa (CUPP) ta umurci sama da jam'iyyu 51 da ke karkashin kungiyar da su ci gaba da gangamin yakin neman zabensu, la'akari da sashe na 99 da ke cikin kundin dokar zabe ta kasa.

Mai magana da yawun kungiyar, Ikenga Ugochinyere, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja wacce ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi inda ya ce sai ranar Alhamis, 21 ga watan Fabreru ne doka ta rufe yakin zaben.

Da ta ke dora hujja da sashe na 99(1) na kundin dokar zaben kasar da ya tanadar da cewar za a dakatar da duk wasu gangamin yakin zabe awanni 24 kafin ranar jefa kuri'a, kungiyar CUPP ta ce zai zama ba dai-dai ba idan har jam'iyyun siyasa suka dakatar da yakin zabensu a ranar 14 ga watan Fabreru alhalin za a fara jefa kuri'a a ranar 23 ga watan Fabreru.

KARANTA WANNAN: Rivers: Za a sake zabe idan har kuka ki sanya mu a ciki - APC ta gargadi INEC

Babbar magana: CUPP ta umurci jam'iyyun da ke karkashinta da su ci gaba da yakin zabe

Babbar magana: CUPP ta umurci jam'iyyun da ke karkashinta da su ci gaba da yakin zabe
Source: Facebook

Sanarwar ta kara da cewa: "Zai zama kamar yiwa doka karan tsaye idan har aka tauye wannan sashe na dokar zaben wacce komai nata a bayyane ya ke baro-baro."

Tun da dai dokar zabe ta ce za a dakatar da yakin zabe awanni 24 kafin ranar jefa kuri'a, to kuwa babu wata hujja da INEC za ta dogara da ita na hana yakin zabe, musamman a tsakanin lokacin da dokar bata hana ba.

"Da wannan muke kira ga dukkanin jam'iyyun da ke cikin wannan kungiya ta mu, da su ci gaba da gudanar da yakin zabensu da kuma wayar da kan masu kad'a kuri'a, tare da tabbatar da cewa al'umma sun zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Nigeria."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel