‘Yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC a jihar Benuwe

‘Yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC a jihar Benuwe

- ‘Yan bindiga sun harbe Boniface Okoloho, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Ohimi da ke jihar Benuwe

- Okoloho dan asalin kabilar Idoma ne da ke rinjaye a yankin jihar Benuwe ta kudu

- A ranar Asabar ne aka dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da INEC ta shirya gudanar wa

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Boniface Okoloho, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Ohimi da ke jihar Benuwe.

An harbe shugaban jam’iyyar ne a jiya, Asabar, a hanyar sa ta koma wa gida bayan halartar wani taron jam’iyyar APC a karamar hukumar Ohimini.

Okoloho dan asalin kabilar Idoma ne da ke rinjaye a yankin jihar Benuwe ta kudu.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da atisaye, Olubunmi Oshoko, ya tabbatar da cewar sun samu labarin cewar ‘yan bindiga sun kai wani hari a karamar hukumar Ohimi.

‘Yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC a jihar Benuwe

Taron gangamin jam'iyyar APC
Source: Depositphotos

Ba zan iya ba ku tabbacin cewar hakan ta faru ba. Mun samu labarin harin ‘yan bindiga daga karamar hukumar amma ba mu da cikakken rahoton abinda ya faru,” kamar yadda Oshoko ya shaida wa jaridar Premium Tomes a wayar tarho a yau, Lahadi.

Sai dai shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Benuwe ta Kudu, Mohammed Hassan, ya tabbatar wa da Premium Times lbarin kisan Okoloho.

DUBA WANNAN: Kisan mutane 66 a Kaduna: El-Rufa'i ya ziyarci kauyukan karamar hukumar Kajuru

Da gaske ne an kasha ma na shugaban jam’iyya na karamar hukumar Ohimi,” kamar yadda ya fada wa Premium Times ta wayar tarho.

Ya bayyana cewar jam’iyyar APC za ta fitar da cikakken bayani a kan kisan nan ba da dadewa ba.

A ranar Asabar ne aka dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da hukmar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta shirya gudanar wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel