Da dumi-dumi: Majalisar dokokin kasa ta dage ranar dawowarta daga hutu

Da dumi-dumi: Majalisar dokokin kasa ta dage ranar dawowarta daga hutu

- Majalisar dokokin kasar ta sanar da dage ranar dawowarta zama wacce ta shirya yi a ranar Talata 19 ga watan Fabrairu zuwa ranar Talata 26 ga watan Fabrairu

- Magatakardar majalisar yace akwai bukatar daga dawowa majalisar sakamakon dage ranar zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da aka daga zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu

Majalisar dokokin kasar ta sanar da dage ranar dawowarta zama wacce ta shirya yi a ranar Talata 19 ga watan Fabrairu zuwa ranar Talata 26 ga watan Fabrairu.

Magatakardar majalisar dokokin kasar, Mista Mohammed Sani-Omolori ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Lahadi, 17 ga watan Fabrairu.

Da dumi-dumi: Majalisar dokokin kasa ta dage ranar dawowarta daga hutu

Da dumi-dumi: Majalisar dokokin kasa ta dage ranar dawowarta daga hutu
Source: Depositphotos

Yace akwai bukatar daga dawowa majalisar sakamakon dage ranar zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokoki da aka daga zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta tafi hutu ne a ranar 24 ga watan Janairu har zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu domin ta samu damar shirye-shirye kan zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki da a baya aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Matakai 5 da INEC ta dauka kafin sabuwar ranar zabe

An kuma tattaro cewa majalisar dattawa ba ta duba dokar rabe-raben kudade ba kafin ta tafi hutu.

Sai dai kuma ta gabatar da dokar mafi karancin albashi zuwa mataki na farko da na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel