Kamfanin Jiragen sama sun yi asarar biliyoyin dukiya sakamakon dage zabe

Kamfanin Jiragen sama sun yi asarar biliyoyin dukiya sakamakon dage zabe

Sakamakon dage zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta yi a jiya Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2019, mun samu cewa wasu kamfanonin jiragen sama sun tafka babbar asara.

Mun samu cewa, a sanadiyar dage babban zaben kasa da hukumar INEC ta yi a jiya Asabar, kamfanonin jiragen sama na Najeriya sun tafka gagarumar asara ta biliyoyin dukiya wajen kudaden shiga da ya kamata su samu ta hanyar sayar da tikitin jiragen sama.

Kamfanin Jiragen sama sun yi asarar biliyoyin dukiya sakamakon dage zabe

Kamfanin Jiragen sama sun yi asarar biliyoyin dukiya sakamakon dage zabe
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, kamfanin jiragen sama na Najeriya ba su ci kasuwar su ba ta jigilar matafiya a fadin kasar daga musamman a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke jihar Legas.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, kamfanonin jiragen sama da wannan biyu-babu ta ritsa da su sun hadar da; Air Peace, Arik Air, Aerocontractors, Dana Air, Azman Air, Max Air, Overland Airways da kuma Medview Airlines.

KARANTA KUMA: Tsakanin Buhari da Atiku: Yadda nasara za ta kasance - Rahoto

Baya ga asara ta rashin sayar da tikitin jigilar matafiya, akwai kuma asara da filayen jiragen sama na kasar nan suka tafka a sakamakon rashin samun kudaden shiga ta hanyar sayar da tikitin jirage ga matafiya.

Rahotanni kamar yadda masu ruwa da tsaki suka bayyana, hukuncin da INEC ta zartar na dage zabe ya yi sanadiyar asarar makudan dukiya ta kimanin Naira biliyan guda yayin da jiragen sama kimanin 90 suka gaza jigilar ma'aikata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel