Zaben 2019: Matakai 5 da INEC ta dauka kafin sabuwar ranar zabe

Zaben 2019: Matakai 5 da INEC ta dauka kafin sabuwar ranar zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta bayyana wasu sabbin matakai da ta ce ta dauka saboda kawo karshen matsaloli da kalubalen da ta fuskanta kafin ta daga zabe.

INEC ta ce za ta tabbatar da ta kawo karshen matsalolin kafin zuwan sabuwar ranar da ta sanya za ta gudanar da zaben yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokokin kasa, wato ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce wadannnan matakai su ne za su zamamafita ga tarin matsalolin da aka fuskanta a baya.

Zaben 2019: Matakai 5 da INEC ta dauka kafin sabuwar ranar zabe

Zaben 2019: Matakai 5 da INEC ta dauka kafin sabuwar ranar zabe
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Nigeria ta yi asarar $1.5bn sakamakon dage zaben ranar Asabar - LCCI

Ga matakan kamar haka:

1. Ranar 17 zuwa 21 ga watan Fabrairu: Za a sake saisaita na’urar tantance masu zabe. Wannan ya zama dole saboda kafin a dage zaben, an saita na’urorin ne yadda a ranar zabe, 16 ga watan Fabrairu ne kadai za a iya sarrafa su. Kenan yanzu sai an saita su, zuwa ranar 23 ga Fabrairu.

2. Ranar18 ga watan Fabrairu: Za a kammala saitata da tantance kayan zabe.

3. Ranar 20 zuwa 21ga watan Fabrairu: za a rarraba kayan zabe a Kananan Hukumomi.

4. Ranar 21 ga watan Fabrairu: Za a yi wa ma’aikatan zabe na wucin gadi wani dan kwarya-kwaryan bitar sanin makamar aiki.

5. Ranar 22 ga watan Fabrairu: Tura jami’an zabe a Cibiyoyin Yin Zabe daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel