Rivers: Za a sake zabe idan har kuka ki sanya mu a ciki - APC ta gargadi INEC

Rivers: Za a sake zabe idan har kuka ki sanya mu a ciki - APC ta gargadi INEC

- Jam'iyyar APC, a jihar Rivers ta bukaci hukumar INEC, da ta tabbata ta sanya 'yan takararta a cikin wadanda za su fafata a zabukan jihar

- APC ta ce bijirewa wannan bukatar zai jawo asarar zaben jihar, kuma tilas ne ga hukumar ta sake wani sabon zabe

- Jam'iyyar ta kuma bukaci al'ummar jihar Rivers da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kad'a kuri'arsu a zaben shugaban kasa

Jam'iyyar APC, a jihar Rivers ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da ta tabbata ta sanya 'yan takararta a cikin wadanda za su fafata a zabukan jihar, tana mai cewa bijirewa wannan bukatar zai jawo asarar zaben jihar, kuma tilas ne ga hukumar ta sake wani sabon zabe.

A kokarinta na ganin hukumar ta cika wannan bukatar tata, jam'iyyar ta ce wakilanta daga jihar Rivers sun shigar da kararraki akan shugaban hukumar ta INEC.

"Zai gurfana ne gaban kotu domin bayyana dalilin da zai hana a garkame shi a kurkuku na kin bin umurnin da kotu ta yi na sanya APC daga cikin masu takara a jihar Rivers," a cewar jam'iyyar cikin wata sanarwa daga daraktanta na watsa labarai a ofishin yakin zaben Tonye Cole, Prince Tonye T.J.T Princewill.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Nigeria ta yi asarar $1.5bn sakamakon dage zaben ranar Asabar - LCCI

Rivers: Za a sake zabe idan har kuka ki sanya mu a ciki - APC ta gargadi INEC

Rivers: Za a sake zabe idan har kuka ki sanya mu a ciki - APC ta gargadi INEC
Source: Twitter

Ya tabbatar da cewa: "Mun shigar da karar ne a jiya saboda munga cewa INEC ta nuna mana ita ba mai zaman kanta ba ce. Ta ya zaka misalta irin tafiyar hawainiyar da take yi akan hukuncin kotu na cewar ta sanya 'yan takararmu a cikin masu fafata zaben jihar? Har yanzu shiru kake ji, hukumar ta hanamu 'yancin da kotu ta bamu.

"Tabbas idan har INEC ta cire mu daga masu yin takara a jihar, za su fuskanci hukuncin da zamu dauka. Zamu iya yin wannan zaben sau daya ko kuma ita INEC ta gudanar da shi har sau biyu. Shari'a dai tana a bayanmu."

Ya godewa al'ummar jihar Rivers akan irin goyon bayan da suke baiwa jam'iyyar tare da bukatarsu akan su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kad'a kuri'arsu a zaben shugaban kasa, kasancewar wanda aka zaba a shugaban kasa shi zai nuna wanda za a zaba a matsayin gwammnan jiha.

"Kar ku damu wai don INEC ta cire mu daga cikin masu fafatawa a zaben jihar, ko sun yi hakan to ya zama tilas a sake wani zaben. Zabe babu mu a ciki ba zabe ba ne. Amma zaben shugaban kasa na nan daram-dam. Dole ne kowacce jiha ta bada goyon bayanta. Hatta mu ma a nan jihar Rivers."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel