Babbar magana: Nigeria ta yi asarar $1.5bn sakamakon dage zaben ranar Asabar - LCCI

Babbar magana: Nigeria ta yi asarar $1.5bn sakamakon dage zaben ranar Asabar - LCCI

- Cibiyar kasuwanci da masana'antu (LCCI) a jihar Legas ta ce Nigeria ta yi asarar akalla $1.5bn, sakamakon matakin da INEC ta dauka, na dage babban zaben kasar

- LCCI ta ce bangaren harkokin da suka shafi ruwa ya samu babbar koma baya da asara saboda dage zaben da INEC ta yi

Cibiyar kasuwanci da masana'antu (LCCI) a jihar Legas ta ce Nigeria ta yi asarar akalla $1.5bn, sakamakon matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dauka, na dage babban zaben kasar.

Da ya ke zantawa da jaridar yanar gizo ta Tribune, babban daraktan cibiyar LCCI, Muda Yusuf ya ce bangaren harkokin da suka shafi ruwa ya samu babbar koma baya da asara saboda dage zaben da INEC ta yi.

A cewar Mr Muda Yusuf, "Dage zaben da INEC ta yi ya jawo babbar asara da koma baya ga kasuwancin kasar. Da yawa daga cikin masu sanya jari sun yi asarar kudadensu, tare da durkushewar tattalin arziki, an yi asarar akalla $1.5bn."

KARANTA WANNAN: El-Rufai ya zabga karya dangane da kisan mutane 66 a Kaduna - CAN, NEMA

Babbar magana: Nigeria ta yi asarar $1.5bn sakamakon dage zaben ranar Asabar - LCCI

Babbar magana: Nigeria ta yi asarar $1.5bn sakamakon dage zaben ranar Asabar - LCCI
Source: Depositphotos

Ya ce saboda zaben ne aka rufe tashoshin jiragen ruwa, inda aka samu tsaiko sosai na sauke kayayyaki da daukar wasu, wanda kuma ya haddasa tsaiko na isar kaya zuwa ga masana'antu, wanda hakan ya jawo babbar asara.

"Kar ku manta da yawan masu shigo da kaya na rancen kudi ne domin shigo da kayan. Idan har ana samun irin wannan tsaikon, to kuwa karshe dan kasuwa zai tashi ba riba babu uwar kudin."

Shugaban LCCI na jihar ta Legas, ya ce: "da yawan ma'aikata a sun samu matsala sakamakon dage zaben, yana mai nuni da cewa da yawan ma'aikata a tashoshin jiragen ruwa na samun kudinsu ne a kowacce rana. Duk awa daya da aka yi ba tare da aiki ba, ba za a biya ma'aikaci kudin aikin ba. Hakika an yi babbar asara a bangaren tashoshin jiragen ruwa na kasar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel