El-Rufai ya zabga karya dangane da kisan mutane 66 a Kaduna - CAN, NEMA

El-Rufai ya zabga karya dangane da kisan mutane 66 a Kaduna - CAN, NEMA

- Kungiyar CAN reshen jihar Kaduna, sun karyata ikirarin gwamnan jihar Nasir El-Rufai na cewar mutane 66 ne 'yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Kajuru

- CAN ta yi ikirarin cewa da sanin gwamnan ya bayar da bayanai na karya domin yaudarar 'yan Nigeria da kuma al'ummar kasashen waje

- Haka zalika, shi ma sanata Shehu Sani, ya yi mamakin dalilin da ya sa ba a dago da batun kai harin a ranar Lahadi ba har sai da aka bari zabe ya zo

Kungiyar al'ummar Kirista ta kasa (CAN) reshen jihar Kaduna, sun karyata ikirarin gwamnan jihar Nasir El-Rufai na cewar mutane 66 ne 'yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Kajuru da ke cikin jihar.

Shugaban kungiyar CAN reshen jihar, Rev. Joseph Hayab, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya yi ikirarin cewa da sanin gwamnan ya bayar da bayanai na karya domin yaudarar 'yan Nigeria da kuma al'ummar kasashen waje.

Ya ce bayanin karyar wanda gwamnan ya bayyana a cikin wata sanarwa a yammacin ranar Juma'a, na da nufin tayar da zaune tsaye a cikin jihar.

KARANTA WANNAN: Rikicin Kaduna: Sakamakon kashe mutane 66, al'ummar Fulani sun yi kaura daga muhallansu

El-Rufai ya zabga karya dangane da kisan mutane 66 a Kaduna - CAN, NEMA

El-Rufai ya zabga karya dangane da kisan mutane 66 a Kaduna - CAN, NEMA
Source: Facebook

Sanarwar da CAN ta fitar ta ce: "Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Mr Samuel Aruwan, ta yi nuni da cewa "an kaddamar da kisan da aka yi a karamar hukumar Kajuru a ranar Juma'a 15 ga watan Fabreru, 2019." Wannan bayanin karyane tsagoransa.

"Mun samu cikakken labarin cewa harin ya faru ne a daren ranar Lahadi, 10 ga watan Fabreru har zuwa ranar 12 ga watan na Fabreru, 2019, da misalin karfe 1 na dare a garin Gindin Gada da ke gundumar Maro, karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna, inda wasu 'yan bindiga suka kaiwa al'ummar kauyen hari tare da kashe mutane 11 a cikin barcinsu.

"Kamar yadda muka samu rahoto an ce an cafke mutane biyu da ke da hannu a kai harin inda aka mikasu ga hukumar 'yan sanda da ke yankin. A tsakar ranar da aka ce an kai harin (kamar yadda yake a cikin sanarwar gwamnan) cewar an saki mai gundumar Kufana, Mr Titus Dauda, da wasu mutane hudu bayan da hukumar tsaron DSS ta gayyyace su.

"Muna kallon wannan a matsayin karyar da ba zata haifar da d'a mai dio ba, wacce kawai zata haddasa rikici a cikin jihar. Wannan karyar da gwmanatin Kaduna ta yi kan harin da aka kai ya kamata mu fahimci cewa akwai wasu shuwagabanninmu da ke son bullo da kalaman batanci da ka iya harzuka 'yan kasar da nufin cimma wasu manufofi na kashin kansu."

Haka zalika, shi ma sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, wanda harin ya faru ne cikin garin da ke cikin mazabar da ya ke wakilta, Shehu Sani, ya yi mamakin dalilin da ya sa ba a dago da batun kai harin a ranar Lahadi ba har sai da aka bari zabe ya zo?

Sani ya kara da cewa bayan faruwar harin, al'ummar garin sunce a shirye suke su gudanar da zabe, suka ki biyewa duk wasu maganganu da ka iya tunzura su, kasancewar sun ce jami'an tsaro sun kwantar da tarzoma a garin, babu wata matsalar tsaro da a yanzu ke wasa da zaman lafiyar su.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel