Tsakanin Buhari da Atiku: Yadda nasara za ta kasance - Rahoto

Tsakanin Buhari da Atiku: Yadda nasara za ta kasance - Rahoto

Gabanin dage babban zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi, a jiya Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019, ya kamata a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki ta tarayyar kasar nan.

Hankoron kujerar shugaban kasa tsakanin dan takara na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari da kuma dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, na ci gaba da tsanani inda masu sharhi akan siyasa suka banbanta ta fuskar ra'ayoyi gami da hasashe.

Tsakanin Buhari da Atiku: Yadda nasara za ta kasance - Rahoto

Tsakanin Buhari da Atiku: Yadda nasara za ta kasance - Rahoto
Source: UGC

Kafar watsa labarai ta duniya, Bloomberg, ta bayyana cewa, tun yayin samun 'yancin kai a 1960, tantance yadda nasara za ta rinjaya tsakanin 'yan takara a yayin zabe abu ne mai matukar wahala sakamakon adadin al'ummar Najeriya da ya kai kimanin miliyan ashirin.

Masu sharhi da nazari akan harkokin siyasa takwas sun rabu gida biyu yayin rinjayar da nasara tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku na jam'iyyar PDP da kuma shugaban kasa Buhari na jam'iyya mai ci ta APC.

Ga yadda wasu manyan kungiyoyi takwas na duniya masu sharhi suka bayyana hasashen su da kiyasta nasara tsakanin manyan 'yan takarar biyu cikin masu hankoron kujerar shugaban kasa 72 a fadin kasar nan yayin babban zaben na bana:

Atiku zai yi nasara

Fitch Solution: Kungiyar Fitch Solution mai tushe a birnin Landan na kasar Birtaniya ta rinjayar da nasara ga Atiku sakamakon gazawar gwamnatin shugaba Buhari na cika alkawurran da ta dauka yayin yakin neman zaben ta a shekarar 2015.

Songhai Advisory: Kamfanin tuntube-tuntube da shawarwari na Songhai mai tushe a birnin Legas na Najeriya, ya ce nasara ta na ga Atiku sakamakon goyon baya da ya samu na manyan tsofaffin sojojin kasar nan da kuma tsofaffin shugabannin kasa da suka hadar da Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida.

Teneo Intelligence: Katafaren kamfanin shawarwari da ke da tushen sa a birnin New York na kasar Amurka, ya kiyasta cewa Atiku zai samu nasara da kimanon kaso 57 cikin 100 na adadin kuri'un al'ummar Najeriya yayin da shugaban kasa Buhari zai samu kaso 42 matukar an gudanar da zabe na gaskiya da adalci.

Verisk Maplecroft: Sakamakon koma bayan tsaro musamman dangane da yadda ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram ke ci gaba da cin karen su ba bu babbaka a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Kamfanin nazari na Verisk mai tushe a kasar Birtaniya ya rinjayar da nasara ga Atiku. Verisk ya kuma ce za a yi gagarumin tashin hankali a fadin kasar nan domin akwai yiwuwar Buhari ba zai sauke daga kujerar sa ba a yayin da sha kasa.

Buhari zai yi nasara

Control Risks: Kamfanin kiyasi da nazari na Control Risks mai tushe a birnin Landan na kasar Birtaniya ya yi hasashen cewa Buhari zai yi nasara da dan kankanin rinyaye akan Atiku. Ya ce rinjayen zai haifar da tashin-tashina a fadin kasar nan da har sai kotu ta shiga tsakani.

Eurasia Group: Kamfanin Eurasia mai nazari da kiyasi da ke a tushe a birnin New York na kasar Amurka, ya ce Buhari zai yi nasara da kimanin kaso 60 cikin 100 na adadin kuri'u a sakamakon rashin rinyayen karfi na jiga-jigan PDP da suka hadar Bukola Saraki da wasu gwamnonin jam'iyyar a Kudu maso Gabashin kasar nan.

NKC African Economics: Jagoran wannan kungiya mai tushe a kasar Afirka ta Kudu, Jared Jeffery, ya ce shugaban kasa Buhari zai nasara da kimanin kaso 80 cikin 100 sakamakon amincin sa ta fuskar yaki da rashawa.

Capital Economics: Kamfanin Capital Economics mai tushe a birnin Landan na kasar Birtaniya da kuma ya shahara akan bincike da nazarin tattalin arziki, ya ce Buhari zai nasara da kankanin kaso na rinjaye. Sai dai kamfanin ya ce duk wanda ya yi nasara tsakanin manyan 'yan takarar biyu zai fuskanci babban kalubale na habaka da ceto durkoson tattalin arzikin Najeriya.

KARANTA KUMA: Abubuwa 4 da dage zabe zai haifar a Najeriya

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel