Abubuwa 4 da dage zabe zai haifar a Najeriya

Abubuwa 4 da dage zabe zai haifar a Najeriya

Biyo bayan dage babban zaben kasar nan da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi a jiya Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2019, masu sharhi akan harkokin siyasa sun bayyana wasu ababe da kasar nan za ta fuskanta a sakamakon hakan.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu yayin bayar da sanarwa dage zabe

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu yayin bayar da sanarwa dage zabe
Source: UGC

A ranar 16 ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa ya shirya gudanar da zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya yayin da ta shirya gudanar da zaben gwamnoni da kujerar 'yan majalisun dokoki na jiha a ranar 2 ga watan Maris.

Kwatsam sa'o'i kalilan gabanin zaben, hukumar INEC ta bayar da sanarwar ta na dage zaben a sakamakon wasu dalilai da ta wassafa da suka hadar da tangarda gami da tasgaro da fuskanta yayin jigila da rarraba kayayyakin zabe zuwa wasu yankuna a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: INEC: Tun da ta kasance haka, za mu ci gaba da yakin neman zabe - Kwankwaso

A yayin da sauyin yanayi na daya daga cikin ababe da suka dakile tashin jiragen sama wajen jigilar kayayyakin zabe tsawon kwanaki uku da suka gabata, masu sharhi akan harkokin siyasa sun bayyana wasu ababe da dage zaben kasar nan ya haddasa.

Hasara ta fuskar tattalin arziki

Hukumar INEC ta batar da makudan kudi wajen shirye-shiryen zabe musamman a ranar jajibirin zaben a bangaren safarar kayan zabe, biyan jami'an ta da kuma biyan alawus ga jami'an tsaro. A halin yanzu hukumar sai ta sake batar da makamancin wannan kudi yayin zaben a mako mai zuwa.

Raguwar kima da mutuncin Najeriya a idon duniya

Duba da yadda ta ake yi ma ta lakabi da madubin nahiyyar Afirka, ba bu shakka kima da mutuncin Najeriya ya zube kasancewar ta kasar da ta yiwa sauran kasashen nahiyyar Afirka fintinkau ta fuskar tattalin arziki.

Hakan ya bayu ne sakamakon yadda kasashen duniya suka zuba idanu domin ganin yadda sakamakon zaben zai kasance, sai dai kwatsam hukumar ta bayar da sanarwar dage zaben har zuwa mako na gaba.

Gazawar hukumar zabe ta kasa

Bayan malala mata dukiya mai tarin yawa, hukumar INEC ta shafe tsawon fiye da shekaru uku tana shirye-shiryen zabe a kasar nan.

Kazalika, shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu cikin wata hira yayin ganawa da manema labarai na BBC a watan Janairun da ya gabata ya bayyana cewa, ba bu yiwuwar daga zaben 2019 domin kuwa hukumar ta kammala duk shirye-shiryen ta da ta faro tun wani lokaci mai tsawo.

Sanyaya gwiwar masu kada kuri'a da ma'aikatan zabe

Ba boyayyen lamari ba ne al'ummar kasar nan da dama a nan gida Najeriya da kuma wadanda ke kasashen ketare sun dawo mahaifar su domin jefa kuri'un su na tabbatar da cikar 'yanci da kishin kasar su.

Kamar yadda shafin jaridar BBC ya ruwaito, zukata da dama na masu zabe a kasar sun karaya, gwiwowi sun sanyaya, jikkunan su sun muta haka ransu ya baci dangane da wannan lamari. Hakan ya sanya wasu suka fusata da cewar sun hakura da jefa kuri'un su a zaben.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel