Zaben 2019: An rufe yakin neman zabe sai kuma 2023 – Inji Shugaban INEC

Zaben 2019: An rufe yakin neman zabe sai kuma 2023 – Inji Shugaban INEC

Mun ji labari cewa hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC ta bayyana cewa an rufe yakin neman zaben shugaban kasa da kuma masu harin kujerar majalisun tarayya a halin yanzu.

Zaben 2019: An rufe yakin neman zabe sai kuma 2023 – Inji Shugaban INEC

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu yace a tsaida kamfe
Source: Facebook

Shugaban hukumar INEC na kasa watau Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa an rufe kofar yawon kamfen na masu takarara kujerar majalisar wakilai da kuma na dattawa watau Sanatoci a babban zaben 2019 na bana.

Mahmood Yakubu, ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da ‘yan jarida bayan hukumar ta dakatar da zaben da aka shirya gudanarwa jiya. A dokar kasa dai ana rufe duk kamfe ne yayin da ya rage saura kwana guda a fara zabe.

KU KARANTA: Dage zabe zai yi wa Jam’iyyar APC mai mulki rana a Najeriya

Wakilin jam’iyyar PDP mai mulki wajen taron da hukumar INEC tayi da masu ruwa da tsaki a zaben bana, Osita Chidoka, ya nemi a bada dama su cigaba da yakin neman zabe tun da an dage zaben kasar har sai zuwa mako mai zuwa.

Sai da shugaban na INEC na kasa, Mahmood Yakubu, ya nuna cewa bai yi na’am da rokon PDP na cigaba da komawa bakin dagar kamfe ba. Shugaban na INEC ya nemi kowace jam’iyya ta dakatar da duk wani kamfe na shugaban kasa.

Osita Chidoka wanda yana cikin ‘yan gaban goshin takarar Atiku Abubakar ya so a ce an ba jam’iyyar PDP ta cigaba da kamfe har sai ana daf da shirya zabe a sabon lokacin da aka ware, a maimakon a zauna a gida gum ba a komai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel