Rashidi Ladoja ya nemi a sauke Shugaban INEC bayan ya daga zabe zuwa mako mai zuwa

Rashidi Ladoja ya nemi a sauke Shugaban INEC bayan ya daga zabe zuwa mako mai zuwa

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, yayi kira ga hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta na INEC da ta fasa amfani da takardun zaben da ta raba a jihohin kasar nan saboda gudun tafka magudi.

Rashidi Ladoja ya nemi a sauke Shugaban INEC bayan ya daga zabe zuwa mako mai zuwa

Babu mamaki takardun zabe su fada hannun jama'a inji Ladoja
Source: Depositphotos

Rashidi Ladoja yayi kira ga hukumar zabe na INEC da cewa ka da tayi amfani da takardun zaben da ta buga a mako mai zuwa, domin kuwa babu mamaki yanzu wasu ‘yan siyasa sun samu takardun don haka za su murde zaben da za ayi.

Cif Ladoja yayi wannan bayani ne a jiya Asabar yana mai caccakar hukumar zaben na Najeriya. Ladoja yayi Allah-wadai da yadda ya kamata ace an shiryawa zaben tun shekaru hudu da su ka wuce, amma a karshe duk aka ji kunya.

Tsohon gwamnan yake cewa ta tabbata cewa babu abin da za a iya tabuka na kirki a Najeriya, yana kuma mai cewa kasashen waje ba za su rika daukar Najeriya da muhimmancin da ya dace a nan gaba ba saboda rashin tanadin INEC.

KU KARANTA: Matukar za a yi zabe na gaskiya Atiku zai yi nasara - Business Day

Cif Rashidi Ladoja yayi kaca-kaca da hukumar zaben inda ya kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya tsige shugabannnin hukumar. Ladoja yace wasu sun taho daga kasar waje ta-ka-nasa amma su ka ji an dage zabe.

Ladoja ya kuma nemi hukumar INEC ta guji amfani da wadannan kayan zabe da aka raba a baya domin kuwa akwai yiwuwar cewa yanzu takardun za a ayi aiki da su, sun fada hannun ‘yan siyasa wanda ke neman murde zaben da za ayi.

Buga wasu sababbin kayan zabe dai zai sa a kara kashe wasu makudan kudi masu yawa kamar tadda tsohon gwamnan na jihar Oyo ya bayyana. Rashifi Ladoja yake cewa wannan abin takaici ne ainun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel