INEC: Tun da ta kasance haka, za mu ci gaba da yakin neman zabe - Kwankwaso

INEC: Tun da ta kasance haka, za mu ci gaba da yakin neman zabe - Kwankwaso

A sakamakon dage babban zaben kasar nan da hukumar INEC ta yi a jiya Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019, wata dambarwa da ta kunno kai ita ce batun ci gaba da yakin neman zabe da wasu 'yan siyasa ke ganin ta gyaru a gare su.

A jiya Asabar, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta dage zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya sakamakon wasu dalilai da ta wassafa na tangarda da ta fuskanta yayin jigilar kayayyakin zabe a wasu jihohin kasar nan.

Sai dai cikin wani jawabi da shugaban hukumar ya gabatar yayin ganawar sa da dukkanin masu ruwa da tsaki, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, jam'iyyu ba za su ci gaba da gudanar da yakin su na neman zabe gabanin sabuwar ranar da ta kayyade na aiwatar da zaben.

INEC: Tun da ta kasance haka, za mu ci gaba da yakin neman zabe - Kwankwaso

INEC: Tun da ta kasance haka, za mu ci gaba da yakin neman zabe - Kwankwaso
Source: Twitter

Wannan lamari ya sanya shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, cikin wata hira yayin ganawa da manema labarai ya ce ba ta sabu ba domin kuwa ka'idar doka shine ana daina yakin neman zaben yayin da rage saura sa'o'i 24 a gudanar da zabe.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, bisa shimfida da madogara ta wannan doka, Kwamared Oshiomhole ya ce jam'iyyar APC za ta ci gaba da yakin neman zabe tun ta kasance an dage zaben har zuwa mako na gaba.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa muka dage zabe - INEC

Kazalika cikin wata hirar sa da manema labarai na BBC, tsohon gwamna kuma wakilin shiyyar Kano ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce sanin kowa ne ka'ida ta dokar hana yakin zabe ita ce sa'o'i 24 gabanin zabe.

Ya ce duk da ba hakan su so ba kuma ba bu wanda ya tursasa hukumar INEC wajen yanke hukuncin ta na dage zabe, za su ci gaba da yakin neman zabe domin girgiza magoya baya tare da zayyana ma su kudirirrika yayin da suka cimma nasara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel