‘Yan bindiga sun kai hari gidan dan takarar majalisar tarayya na APC

‘Yan bindiga sun kai hari gidan dan takarar majalisar tarayya na APC

Dan takarar majalisar tarayya a mazabar Ika da ke jihar Delta, Mista Sebastian Okoh, ya tsallake rijiya da baya yayin da ‘yan bindiga su ka kai wani mummunan hari tare da yin ruwan alburusai a gidan sa.

Da ya ke bayanin yadda lamarin ya faru, Okoh ya ce yana cikin gida tare da iyalin sa lokacin da ‘yan bindigar su ka fara ruwan alburusai zuwa cikin gidan, lamarin da ya ce ya jawo lalata ma sa motoci da ragowar kayayyaki da ke gidan sa.

Okoh, tsohon hadimin gwamnan jihar Delta da ya ajiye mukamin sa ya kuma canja sheka daga PDP zuwa APC, ya ce an kai ma sa harin ne domin razana shi daga niyyar sa ta kwato wa jama’a ‘yanci.

‘Yan bindiga sun kai hari gidan dan takarar majalisar tarayya na APC

Yakin neman zaben APC
Source: Facebook

Da ya ke yi wa Allah godiya bisa kare shi tare da iyalin sa, Okoh ya bukaci masoya da magoya bayan sa da su kwantar da hankalin su, sannan ya kara da cewa akwai dalilin da ya saAllah ya tserar da shi.

Dan takarar ya bayyana cewar tun kafin a kai ma sa harin ya sanar da rundunar ‘yan sanda a kan ganin motsin wasu bakin fuska a yankin da gidan sa ya ke.

DUBA WANNAN: Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari, ya hakura da takara

Jama’ar yankin Umende da gidan Okoh ya ke sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin nuna fushin su a kan yunkurin hallaka dan siyasar.

Sai dai rundunar ‘yan sanda karkashin jagorancin ACP Cordelia Ikejiani t ziyarci gidan Okoh tare da daukan alkawarin gudanar da bincike a kan harin da aka kai ma sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel