Dalilin da ya sa muka dage zabe - INEC

Dalilin da ya sa muka dage zabe - INEC

A jiya Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta a Najeriya, INEC, ta shirya gudanar da babban zaben kasa na kujerar shugaban kasa da kuma na 'yan majalisun dokoki na tarayyar kasar nan.

Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, a jiya Asabar ya fayyace dalilai da suka sanya hukumar ta yanke hukuncin ta na dage babban zaben tare da sauya ranakun gudanar sa a fadin kasar nan.

Cikin dalilai da jagoran hukumar ya wassafa a wata hirar sa yayin ganawa da dukkanin masu ruwa da tsaki, Farfesa Yakubu ya ce ba bu wata tangarda a siyasance ko kuma rashin tsaro da ta sanya hukumar ta yanke hukuncin dage babban zabe na kasa.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Source: Depositphotos

Farfesan ya ke cewa, hukumar ta fuskanci babbar barazana gami da tangarda a bangaren jigila da rarraba kayayyakin zabe cikin wasu lunguna da sako da dole za a ribace su yayin gudanar da zabe a fadin kasar nan.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar INEC ta samu tangarda musamman a bangaren jigilar takardun kada kuri'a tsawon kwanaki uku da suka gabata sakamakon matsala ta sauyin yanayi na hazo da ya hana jirage tashi.

Baya ga tangarda ta sauyin yanayi, Farfesa Yakubu ya ce akwai kuma annoba ta wutar gobara da ta lakume kayayyakin zabe da ke wasu ma'aikatu uku na rassan hukumar INEC cikin wasu kananan hukumomi a jihar Abia, Anambra da kuma Filato.

KARANTA KUMA: Muhimman ababe da ya kamata ku sani game da zaben 2019

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, wannan manyan dalilai sun yi tasiri kwarai da aniyya wajen kawo tangarda a kasar nan da ya sanya hukumar INEC ta dage zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kazalika hukumar ta dage zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki na jiha da shirya gudanarwa a ranar 2 ga watan Maris inda ta sauya shi zuwa ranar 9 ga watan na Maris na shekarar na ta 2019 da muke ciki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel