Allah Sarki: Kwanan wani babban yaron tsohon Gwamnan Edo sun kare

Allah Sarki: Kwanan wani babban yaron tsohon Gwamnan Edo sun kare

- Daya daga cikin ‘Ya ‘yan tsohon Gwamna Cif Lucky Igbinedion ya rasu

- Lucky Igbinedion ya rasa wani babban ‘Dan sa ne a hadarin mota jiya

- Osaretin Igbinedion da wani ‘Dan uwan sa sun rasu ne a Kasar Amurka

Allah Sarki: Kwanan wani babban yaron tsohon Gwamnan Edo sun kare

Yaron tsohon Gwamnan Edo yayi hadarin mota a Amurka
Source: Facebook

Ba da dadewa bane mu ka samu labari cewa tsohon gwamnan jihar Edo watau Lucky Igbinedion, ya rasa Iyalin sa a wani hadarin mota da ya rutsa da su. Wannan labari ya zo mana ne ta bakin wani na kusa da tsohon gwamnan.

Daya daga cikin manyan ‘ya ‘yan Lucky Igbinedion, da kuma wani Yaron ‘dan uwan tsohon gwamnan sun mutu a wani mummunan hadarin mota da su kayi a Ranar Asabar da tsakar dare. Wannan abu ya faru ne a Amurka.

KU KARANTA: An gano takardun yarinyar nan da Boko Haram su ka sace

Osaretin Igbinedion, wanda shi ne na-biyu cikin ‘ya ‘yan tsohon gwamnan jihar Edo Lucky Igbinedion, da kuma wani ‘Dan uwan sa Esosa Oyemwense, sun bakunci lahira ne bayan da motar su ta aukawa wani mai gingimari.

Wannan abu maras dadi ya faeu ne a cikin birnin Texas na kasar Amurka da kimanin karfe 3:00 na dare. Jefferson Uwoghiren wanda da alamu yana da kusanci da iyalin tsohon gwamnan kasar ne ya bayyana mana wannan jiya.

Osaretin Igbinedion yayi Digirin sa na farko ne a harkar kasuwanci da tattalin arziki a jami’ar Pittsburgh, sannan kuma yayi Digiri na biyu a makarantar Northeastern University da ke Garin Boston a kan fannin kasuwancin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel