Shugaban Majalisar Najeriya yana da cewa game da fasa yin zabe da aka yi

Shugaban Majalisar Najeriya yana da cewa game da fasa yin zabe da aka yi

Mun ji labari cewa hugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, yayi magana game da dakatar da zabe da aka yi a kasar nan. Bukola Saraki yace wannan ba laifin kowa bane illa gwamnatin Najeriya.

Shugaban Majalisar Najeriya yana da cewa game da fasa yin zabe da aka yi

Bukola Saraki yace INEC ba ta kyautawa mutanen Najeriya ba
Source: Depositphotos

Darektan na yakin neman zaben Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP mai adawa yace dakatar da zaben da aka yi ya taba ma’aikata da kuma masu yi wa kasa hidima da ma ‘yan kasuwa da su ka sa ran za su yi aiki a lokacin zaben.

Bukola Saraki yace abin takaici ne babba da aka dakatar da zabe sai wani mako. Shugaban majalisar kasar yayi kira kuma ga hukumar zabe mai zaman kan-ta, ta tabbatar an yi zaben a makon gobe kamar yadda ta tsara a yanzu.

KU KARANTA: An kone motocin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom

Haka zalika, Bukola Saraki ya nemi mutanen Najeriya cewa da ka da su karaya, su shirya su fita su kadawa PDP kuri’ar su a ranar zabe mai zuwa. Saraki ya kuma nemi al’umma su gujewa dabar siyasa da duk wani tashin-tashina.

Har wa yau, shugaban majalisar dattawan na Najeriya ya koka da yadda ‘yan kasuwa su ka shiga cikin wani hali a dalilin dage wannan zaben. Haka kuma masu yi wa kasa hidima wanda su ka shirya tsara zaben sun wahala a banza.

Abin da yayi wa Sanatan ciwo shi ne bari da aka yi sai tsakar dare kafin a sanar da matakin dage zaben. Saraki yace wannan ba zai sa jama’a su karaya wajen ganin sun tika gwamnatin shugaba Buhari da kasa a mako mai zuwa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel