Shugaba Buhari na kokarin dakatar da Shugaban INEC – Inji CUPP

Shugaba Buhari na kokarin dakatar da Shugaban INEC – Inji CUPP

Mun ji labari cewa kungiyar hadakar jam’iyyun adawa na Najeriya watau CUPP ta bayyana cewa shugaba Buhari yana yunkurin dakatar da shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, daga matsayin sa.

Shugaba Buhari na kokarin dakatar da Shugaban INEC – Inji CUPP

Buhari na neman dakatar da Farfesa Mahmood Yakubu - CUPP
Source: UGC

Kakakin kungiyar ta ‘yan adawa, Imo Ugochinyere yake cewa an shirya korar Mahmood Yakubu daga bakin aiki inda ake neman maye gurbin sa da Amina Zakari wanda ita ce mafi girma a cikin kwamishinonin hukumar INEC.

Ugochinyere yake cewa gwamnatin Buhari tana neman tayi amfani da dakatar da zaben da aka yi a matsayin dalili na yin waje da shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC, domin a nada Hajiya Amina Zakari.

KU KARANTA: Atiku ya kwancewa Buhari, APC da INEC zani a kan dage zabe

Mai magana da yawun bakin na kungiyar CUPP yayi tir da yadda shugaban kasar yayi gum game da yadda jami’an tsaro da babban bankin CBN na kasa wadanda su ke karkashin sa su ka rika kawowa INEC cikas kwanan nan.

Kungiyar tayi ikirarin cewa shugaban na INEC ya ki amincewa da a gudanar da zabe a wasu wurare tare da dakatar da zaben wasu yankin jiya, wanda zai bada damar a tafka magudi, don haka ake kokarin a tsige sa daga kan kujerar na sa.

CUPP ta gargadi gwamnatin shugaba Buhari ta guji aikata wannan aiki domin kuwa dokar kasa ba ta bata dama ba. Kwanan nan ne shugaban kasar yayi waje da babban Alkalin Najeriya wanda kungiyar tace ya sabawa tsarin mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel