An kone motocin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

An kone motocin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

Wasu fusattatun matasa da ba san ko su wanene ba sun kone motoccin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ake amfani dashi wurin jigilar matasa masu yiwa kasa hidima da ke aikin zabe a karamar hukumar Obot Akara da ke jihar Akwa Ibom.

An tafka wannan mummunan aikin ne tun kafin hukumar zabe INEC ta sanar da cewa an dage zaben zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Rahotanni da muka samu daga Tvc News na cewa motoccin uku da aka kone suna dauke da kayayakin zabe ne a hanyarsu da zuwa karamar hukumar Obot Akara kuma an sari direban motan da wasu fasinjoji.

Har ila yau, rahoton ya kuma ce an kuma kashe mutane biyu. Wannan abin ya jefa matasa masu yiwa kasa hidiman cikin hadari sosai.

Ga hotunan motocin na a kasa:

An kone motoccin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

An kone motoccin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

An kone motoccin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

Motoccin hukumar INEC da aka kone a jihar Akwa Ibom
Source: Twitter

An kone motoccin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

Motoccin hukumar Zabe na kasa INEC ta wasu bata gari suka kone a jihar Akwa Ibom
Source: Twitter

An kone motoccin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

Motoccin INEC ta wasu bata gari suka kone a jihar Akwa Ibom
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel