'Dage zabe da INEC tayi wani mummunan shiri ne kan mulkin Buhari'

'Dage zabe da INEC tayi wani mummunan shiri ne kan mulkin Buhari'

- Yan Najeriya mazauna Europe sunce dage zabe da akayi abune da baiyi dadi ba da kuma bita da kulli da akewa gwamnatin Buhari

- Mazauna Europe da dama sun baro kasar sun taho Najeriya dansu samu damar kada kuri'ar su

- Da yawa daga cikin su sunce ba dage zaben ne ya bata musu rai ba face sanarwa da akayi a kurarren lokaci

Zabe: Bai kamata a bari APC

Zabe: Bai kamata a bari APC
Source: UGC

Yan Najeriya mazauna Europe sun bayyana dage zaben shekara ta 2019 da akayi da wani abu mara dadi da kuma bita da kulli da akewa gwamnatin Buhari.

Sun maida martani bisa dage zaben shugaban kasa,yan majalisun tarayya,gwamnoni da kuma yan majalisar jiha da akayi.

An tsara gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar daga baya kuma hukumar zabe ta kasa(INEC) ta fito ta bada sanarwar dage gudanar da zaben zuwa 23 ga watan na gwamnoni kuma 9 ga watan Mayu.

Mazauna kasar sunyi wannan jawabi ne ta wayar tarho inda suka bayyana rashin jindadin su bisa ga wannan abu.

GA WANNAN: Yadda Boko Haram suka kai mana hari a jiya - Gwamna Shettima

Mr Bayo Machael wanda ya kasance ciyaman na kungiyar nan ta NIDO yace hukuncin da INEC ta yanke baiyi dadi ba.

Wani mai harkar kididdiga a bangaren siyasa dake kasar London Mr Godwin Azu ya bayyana dage zaben da akayi a matsayin "Abun zargi da kuma rashin amincewa".

Mutane sunyo tattaki daga Europe zuwa Najeriya dansu gudanar da zaben su amma daga karshe abinda aka yanke.

Hukumar zabe tana gudanar da shirye shiryen zabe tsayin shekara Hudu wanda idan har tasan cewa zata dage zaben meya hana ta sanar tun da 1 ga watan Fabrairu dan bawa mutane damar canja tsare-tsaren su.

Wadanda sukayi magana daga kasar Germany,Spain da kuma Italy sunce ba dage zaben ne ya bata ransu ba face lokacin da aka sanar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel