Yanzu-Yanzu: Abubuwa masu fashewa na can suna tashi a Enugu

Yanzu-Yanzu: Abubuwa masu fashewa na can suna tashi a Enugu

- Abubuwa masu fashewa suna can suna fashewa a jihar Enugu

- Ba wannan ne karo na farko ba da aka samu fashe fashen abubuwa a ranar zabe a jihar

- Mutane suna ta guje guje dan ganin sun tsira da rayukan su

Yanzu-Yanzu: Abubuwa masu ffashewa na can suna tashi a Enugu

Yanzu-Yanzu: Abubuwa masu ffashewa na can suna tashi a Enugu
Source: Facebook

A yammacin ranar Asabar ne abubuwa masu fashewa suke ta tashi a jihar Enugu bayan an dage zaben shugaban kasa dana yan majalisu.

Mutum daya ya samu rauni inda wani dutse ya taso ya sameshi a kasuwar Oye Omene.

An bayyana cewa tashin abun ya janyo guje guje a cikin al'umma inda kowa yake ta kansa.

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: UGC

Duk da cewa har zuwa yanzu babu wani rahoto daya bayyana cewa an samu asarar rayuka face mutum daya daya samu rauni.

Hukumar yan sandan jihar ta Enugu sun tabbatar da afkuwar lamarin inda sukace ba wani gagarumin fashewar abu bane.

GA WANNAN: Gani Adams na OPC a kasar Yarabawa, yace a zabi mai tsoron Allah a zabukan 2019

SP Amaraizu yace an samu wannan fashewar abu ne sanadiyyar (Knock out) wanda aka sanya dan firgita mutane dan karsuyi zabe.

Amaraizu yace hukumar yan sanda ta halarci wajen sannan ta umarci mutane dasu cigaba da gudanar da al'amuran su ba tare da wata fargaba ba.

Idan zamu iya tunawa jihar Enugu tana da tarihin tashin ababen fashewa a duk ranar zabe.

A shekara ta 2015 an samu irin hakan a makarantar firamare ta WTC a ranar zabe.

Sannan hakan ta kara faruwa a zaben gwamnoni na karshe da aka gudanar a watan Nuwamba shekara ta 2016 a Coal Camp dake jihar ta Enugu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel