An zargi Obasanjo da INEC da hada kai don taimakawa PDP da dage zabe

An zargi Obasanjo da INEC da hada kai don taimakawa PDP da dage zabe

- NFN ta zargi tsohon shugaban kasa Obasanjo da shirin magudin zabe

- Shugaban ya hada kai ne da tsohon mataimakin shi Atiku Abubakar, gwamna Nyesome Wike da sauran mukarraban su

- Yin hakan ne yasa hukumar zabe mai zaman kanta ta yi gaggawar dage zaben shugaban kasa da na yan majalisar kasar nan

An zargi Obasanjo da INEC da hada kai don taimakawa PDP da dage zabe

An zargi Obasanjo da INEC da hada kai don taimakawa PDP da dage zabe
Source: Instagram

An zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da yunkurin magudi a zaben shugabancin kasa da ak daga inda ya hada kai da wasu jami'an hukumar zabe mai zaman kanta.

Wasu masu ruwa da tsaki, karkashin NFN ne sukayi zargin nan a cikin maganar su ga manema labarai a Abuja a jiya.

Shirin zaben shugaban kasar da na yan majalisar dattawa ya samu nakasa ne sakamakon yunkurin da wasu sukayi na magudi wanda hakan tasa dole hukumar ta dage zaben.

Kamar yanda shugaban NFN Alhaji Abubakar Tsav, tsohon kwamishinan korafi, yace Obasanjo na a sahun gaba a jawo wannan nakasa.

Tsav yace tsohon shugaban kasar ya kammala shirin shi na magudin zaben tare da hadin kan tsohon mataimakin shi Atiku Abubakar da gwamna Nyesome Wike.

"Sharrin da Obasanjo, Atiku, Wike da sauran su suka shiryawa Najeriya na da yawa. Kamar yasan yan Najeriya na shirye da suyi zaben da zai tozarta shi da kuma biyayyar shi ta karya, a don haka ne ya shirya tsaf don murde zaben," inji Tsav.

GA WANNAN: An gano sakamakon jarrabawar karshe da yarinyar nan mai kwazo Leah tayi, kafin bautar Boko Haram

A kurarren lokaci ne hukumar zabe ta gano shiryayyiyar manakisar da suke shiryawa don haka ne shugaban hukumar yayi saurin dage zaben da burin cewa zasu shawo kan sharrin da su Obasanjo ke shiryawa don hana nagartaccen zabe. Kafin nan anyi kira da dama ga wadannan mutanen don su gujewa duk wani yunkurin su na jefa kasar nan cikin hargitsi da hayaniya,"

"A maimakon su gyara munanan abubuwan da suka aikata a da, amma sai suke zargin gwamnati mai mulki da laifin shirya magudi. Suna hada baki da magoya bayan su na kasashen waje dasu ce zaben ba ayi mai nagarta ba. Bayan sune suke kokarin murkushe zaben da kasar baki daya."

Shugaban yayi kira ga yan Najeriya dasu maida hankali wajen zaben shuwagabanni na gari tare da tunanin irin Najeriyar da suke so nan gaba yayin zaben.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel