Dage zaben 2019: Kar ku ga laifin INEC - CLO

Dage zaben 2019: Kar ku ga laifin INEC - CLO

- Kungiyar kare hakkin al'umma ta Civil Liberty Organisation ta yi kira ga 'yan Najeriya su yiwa INEC uzuri game da dage zabe

- Kungiyar ta ce wannan ba shine karo na farko da aka fara dage babban zabe a Najeriya ba duk da cewa abin ya bawa mutane mamaki

- Kungiyar ta yi kira ga 'yan Najeriya su bawa hukumar INEC hadin kai domin ta samu ikon gudanar da sahihiyar zabe

Shugaban kungiyar kare hakkin al'umma ta Civil Liberty Organisation (CLO) reshen jihar Bayelsa, Mr Nengi James ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta magance kalubalen da ke hana ta gudanar da sahihiyar zabe.

Dage zaben 2019: Kar ku ga laifin Hukumar INEC - CLO

Dage zaben 2019: Kar ku ga laifin Hukumar INEC - CLO
Source: Original

DUBA WANNAN: Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

A sanyin safiyar ranar Asabar ne kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta sanar da cewa INEC ta dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Fabrairu da na ranar 2 ga watan Maris inda aka dage zuwa 23 ga watan Fabrairu da 9 ga watan Maris.

James wanda har ila yau shine shugaban kungiyar sa ido a kan zabe na yankin Kudu maso Kudu ya yi wannan jawabin ne a ranar Asabar yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

"Kada 'yan Najeriya su ga laifin Hukumar INEC saboda wannan ba shine karo na farko da ake dage zabe a Najeriya ba.

"Duk da cewa labarin dage zaben ya bamu mamaki, abinda ya faru ya riga ya faru, saboda haka ya dace mu bawa INEC hadin kai domin ganin demokradiyyar mu ta inganta a Najeriya," inji shi.

Mutane da kungiyoyi daban-daban suna ta bayyana ra'ayoyinsu a kan dage zaben ta kafafen yada labarai da na sada zumunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel