Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ce ta sa aka dage zabe - PDP

Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ce ta sa aka dage zabe - PDP

Shugabanin babban jam'iyyar adawa na PDP sun yi ikirarin cewa fadar shugaban kasa ce ta kitsa shirin dage babban zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC tayi a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Tayi ikirarin cewa fadar shugaban kasa ce da shirya dage zaben sai dai ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zai sha kaye nan da kwanaki kadan.

Jam'iyyar adawar ta kuma yi ikirarin cewa har yanzu fadar shugaban kasar tana cigaba da shirin yadda za ta janyo wasu cikas ga hukumar zabe INEC ta yadda ba za a gudanar da zabukkan a rana guda ba.

Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ce ta sa aka dage zabe - PDP

Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ce ta sa aka dage zabe - PDP
Source: UGC

DUBA WANNAN: Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mr Kola Ologbondiyan a cikin jawabin da ya yi a taron manema labarai da jam'iyyar ta kira domin tofa albarkacin bakin ta a kan dage zaben.

A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja inda zai hallarci wani taron da shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shirya zaben na Najeriya.

Ana sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ne a ranar 23 ga watan Fabrairu yayin da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi kuma za a gudanar da shi a ranar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel