PDP da APC ne suka janyo dage zaben nan, dan takarar shugaban kasa Moghalu yayi zargi

PDP da APC ne suka janyo dage zaben nan, dan takarar shugaban kasa Moghalu yayi zargi

- Dan takara a jam'iyar YPP yayi kira ga yan Najeriya dasuyi hakuri bisa dage zabe da akayi

- Yace an dage zaben ne saboda gazawar jam'iyar PDP da APC

- Hukumar zabe ta INEC ta dage zaben shugaban kasa dana yan majalisu da aka shirya gudanarwa a yau zuwa sati mai zuwa

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Source: Instagram

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Young progressive party(YPP) Kingsley Moghalu ya shawarci yan Najeriya da suyi hakuri bisa dage zaben da akayi.

A ranar Asabar Mr Moghalu ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta dage zaben ne saboda gazawar jam'iyar PDP da APC.

Ya kara da cewa an dage zabe a shekara ta 2015 karkashin gwamnatin jam'iyar PDP inda yan Najeriya sukayi shiru suka kudirta canja sheka ta hanyar zabar wata jam'iyar.

INEC ta dage gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisu wanda aka shirya gudanarwa a yau din nan zuwa sati na sama,yayin da ta dage zaben gwamnoni da yan majalisar jiha daga 2 ga watan Mayu zuwa 9 ga wata.

Mr Moghalu ya bayyana jin kunyar sa bisa ga wannan lamari da ya afku sannan yace wannan abun kunya ne matuka.

GA WANNAN: Yadda ake sace namun dajin Najeriya a sayar da makudan daloli a kasashen ketare

"An janyowa dalibai 'yan makaranta canje-canje a sha'anin karatun su haka ma bangaren tattalin arziki zai tabu saboda wannan abu".cewar Moghalu

"Mutane da dama sun baro guraren da suke zaune sun taho dan kawai su samu damar kada kuri'ar su amma kuma an dage zaben".

Daga karshe ya mika godiyar sa ga magoya bayan shi da kuma masoyan jam'iyar ta YPP bisa goyan bayansu a gareshi,sannan ya kara da cewa su tabbatar da wannan zaben zabe ne na share musu hawaye.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel