Bani da masaniyar za'a dage zabe, shugaba Buhari ga masu zargin ko shi yasa a dage

Bani da masaniyar za'a dage zabe, shugaba Buhari ga masu zargin ko shi yasa a dage

- Shugaba Buhari ya dawo Abuja don ci gaba da hutu

- Yace shima ya kadu da jin labarin

- Wasu sun zarge shi da dakatar da zabe

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Source: Facebook

'Kamar yadda kowa ya kadu haka nima naji labarin bagatatan.na dage zaben yau da safen nan, nayi mamaki matuka da aka dage zaben' inji Shugaba Buhari, kan dage zabe da mako daya da INEC tayi da asubahin nan.

Sanarwar ta fito daga hannun mai hidimta masa kan harkokin yada labaru, Garba Shehu, daga Daura, jin kadan kafin shugaban ya baro garin nasa zuwa Abuja babban birnin Tarayya.

Wasu dai musamman daga PDP na cewa ai gani yayi zai fadi shi yasa ma yace a dage zaben, musamman ganin gwamnatoci a baya sunyi hakan suma.

GA WANNAN: Bincike: Yawan 'yan Najeriya dake cikin matsanancin Talauci ya kai 91m

INEC din dai tace matsalar aikatau da safara ce ta sanya ta dage zaben.

Da yawa daga cikin 'yan Najeriya dai, da ma baki da suka zo basu ji dadin wannan lamari ba, kuma sunje soshiiyal midiya don nuna takaicinsu.

Wasu ma cewa sukayi shirin magudi ake yi.

Yanzu dai masu kananan sana'a sun tafka asara sosai kan wannan dage zabe da aka yi, ana kuma sa rai shugaban Najeriya, bayan jin bahasi daga INEC, zai sake kwantar wa da duniya hankali a daren yau.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel