Bayan dage zabe an sake bude iyakokin Najeriya na wucen gadi

Bayan dage zabe an sake bude iyakokin Najeriya na wucen gadi

- Dage zaben ya jawo-cece-kuce

- An maida Najeriya shashashar kasa

- Anyi asarar lokaci da kudade kan dage zabe

Bayan dage zabe an sake bude iyakokin Najeriya na wucen gadi

Bayan dage zabe an sake bude iyakokin Najeriya na wucen gadi
Source: Twitter

Hukumomi masu kula da shige-da-fice a iyakokin Najeriya, sun sanar da cewa sun bude iyakokin kasar wadanda suka rufe a baya don shirin shiga manyan zabuka, kamar yadda ake yi a al'adance, domin tsaro, da kiyayar bakin haure.

Muhammad Babandede , The Comptroller-General of Immigration, shine ya bada wannan sanarwa dazu ga manema labarai a Abuja.

GA WANNAN: Har a kotu, Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile

Sanarwar tace: Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, ya bada odar a sake bude iyayoykin kasarnan na kasa, masu makwabtaka da kasashen Kamaru, Chadi, Benin da Nijar domin komawa harkokin yau da kullum.

A bisa al'ada, ana rufe wadannan iyakoki lokuta-lokuta, ko don zabe, ko tsaro, ko ma juyin mulki in anyi.

Wannan na nufin sai makon gobe za'a sake rufe iyakokin domin fuskantar zaben 2019 na shugaban kasa, in INEC ta ce ta shirya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel