Yanzu-yanzu: Boko Haram sun tayar da Bom a masallacin Maiduguri

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun tayar da Bom a masallacin Maiduguri

Wasu mambobin kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kai mumunan harin Bom wata masallaci a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ranan Asabar, 16 ga watan Febrairu, 2019, akalla mutane 11 sun rasa rayukansu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Borno, Damien Chukwu, ya tabbatar da hakan inda yace hakan ya faru ne misalin karfe 5:40 na asuba.

Yace yan kunar bakin waken tare da wani dan bindiga sun shiga masallacin dake kayen Kushari ne kusa da CBN quaters.

Yace: "Yayinda muka ga abinda ya faru a wajen misalin karfe 0540hrs. Wasu yan bindiga dake zargin yan Boko Haram ne sun shiga Gwozari/Kushari a unguwar Polo, ina sukayi harbe-harbe kuma suka tayar da bama-bamai."

"Mutane 11 tare da yan ta'addan 3 suka rasa rayukansu yayinda mutane 15 sun jikkata kuma suna asibitin Maiduguri yanzu."

Wannan hari na zuwa kimanin kwanaki hudu ne da yan ta'addan suka budewa motar gwamnan jihar, Kashim Shettima, wuta.

Jami'in soja daya, masu farar huka biyu suna rasa rayukansu a ranan Laraba yayinda yan Boko Haram suka budewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wuta a yankin Borno ta Arewa yayinda yaje yakin neman zabe.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da hakan ga jaridar The Nation. Ya ce an yan ta'addan sun kai farmakin ne a Gajibo, karamar hukuma Dikwa na jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel