Dage zaben 2019: INEC za ta gana da masu ruwa da tsaki da misalin karfe 2 na rana

Dage zaben 2019: INEC za ta gana da masu ruwa da tsaki da misalin karfe 2 na rana

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za ta gana da masu ruwa da tsaki a harkokin zaben kasar da misalin karfe biyu na rana domin tattaunawa kan batun da ya shafi matakinta na dage zaben shugaban kasa da kuma sauya lokutan gudanar da zaben.

Hukumar INEC dai zata gana da masu ruwa da tsakin ne, bayan da ta yanke hukuncin dage babban zaben kasar har zuwa mako mai zuwa, a cikin kasa da awanni biyar kafin fara zaben.

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa dage zaben ya biyo bayan kyakkyawan nazari da kuma dabaru na gudanar da aiki, da kuma kudurinta na gudanar da sahihin zabe, wannan ne ya sa hukumar ta ga cewa idan har ta gudanar da zaben a halin da ake ciki, lamarin ba zai yi karshe mai kyau ba.

KARANTA WANNAN: Bar murna karenka ya kama kura - Atiku ya caccaki Buhari kan dage zabe

Dage zaben 2019: INEC za ta gana da masu ruwa da tsaki da misalin karfe 2 na rana

Dage zaben 2019: INEC za ta gana da masu ruwa da tsaki da misalin karfe 2 na rana
Source: Facebook

Ya ce dage zaben zai baiwa hukumar damar magance duk wasu matsaloli da ka iya tasowa yayin zaben da kuma tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin tsari ta yadda kowa zai amince da sakamkonsa.

"Hakika wannan mataki ne mai wuyar dauka, amma yin hakan ya zama wajibi domin ganin cewa hukumar ta gudanar da sahihin zabe da zai tabbatar da dorewar demokaradiyyar kasar." a cewar sa.

"Hukumar a yanzu ta dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabreru, 2019.

"Haka zalika, zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokoki da kuma na cikin babban birnin tarayya Abuja zai gudana a ranar Asabar 9 ga watan Maris, 2019."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel