Bar murna karenka ya kama kura - Atiku ya caccaki Buhari kan dage zabe

Bar murna karenka ya kama kura - Atiku ya caccaki Buhari kan dage zabe

- Alhaji Atiku Abubakar, ya ce dage zaben da INEC ta yi, makircin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na fusata 'yan Nigeria

- Atiku ya yi nuni da cewa duk da INEC ta canja lokacin zaben, hakan ba wai yana nufin cewa akwai mai ikon canja kaddarar sakamakon zaben ba

- Atiku ya yi kira ga daukacin 'yan Nigeria da su kasance masu rungumar zaman lafiya tare da jajurcewa domin fitowa kwansu da kwarkwatarsu a makon mai zuwa

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce dage zaben da INEC ta yi, makircin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na cirewa 'yan Nigeria sha'awar fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kad'a kuri'arsu kasancewar ya san zai sha kasa a zaben.

Da wannan ne ya sa Atiku ya yi nuni da cewa duk da INEC ta canja lokacin zaben, hakan ba wai yana nufin cewa akwai mai ikon canja kaddarar sakamakon zaben ba.

A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, cikin martanin da ya mayar kan canja lokacin zaben zuwa mako mai zuwa, Atiku ya yi kira ga daukacin 'yan Nigeria da su kasance masu rungumar zaman lafiya tare da jajurcewa domin fitowa kwansu da kwarkwatarsu a makon mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Na gamsu da hukuncin INEC na dage zabe - Wani minista ya yi caccaki 'yan adawa

Bar murna karenka ya kama kura - Atiku ya caccaki Buhari kan dage zabe

Bar murna karenka ya kama kura - Atiku ya caccaki Buhari kan dage zabe
Source: Depositphotos

Sanarwar ta ce: "Gwamnatin Buhari ta samu isasshen lokaci da kudi na shiryawa zaben kasar, kuma 'yan Nigeria sun zaku su kad'a kuri'unsu a ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru, 2019. Sai dai suna tunanin cewa dage zaben zai fusata wasu 'yan Nigeria har su ce sun fasa zaben gaba daya. Ya zama wajibi 'yan Nigeria su basu kunya ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatarsu wajen kad'a kuri'unsu a ranar 23 ga watan Fabreru da ranar 9 ga watan Maris

"Sanin cewa 'yan Nigeria sun gaji da irin salon mulkinsu, ya sa suka dage da bin duk wasu hanyoyi na ganin sun ci gaba da kasancewa a karagar mulkin kasar domin gujewa jin kunyar shan kaye.

"Da wannan na ke kira ga daukacin 'yan Nigeria da su kasance masu hakuri. Mun jure bakar wahalar da muka sha karkashin wannan gwamnati na tsawon shekaru hudu. Za mu iya jure kwanaki bakwai domin tunkude gwamnati mai ci ta hanyar kuri'unmu."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel